Lagos Third Mainland Bridge: Yadda rufe wani sashe na Gadar ya shafi sufuri

Asalin hoton, BBC/Ayo Bello
- Marubuci, Daga Ayo Bello
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
- An wallafa
Mazauna Lagos, birni mafi shahara a Najeriya - da Afrika - sun dade suna fama da karuwar matsalolin cunkoson ababen hawa fiye da yadda aka sani saboda rufe wani sashe na hanyar babbar gada ta uku a ƙwaryar birnin wato 'Third Mainland Bridge'.

Asalin hoton, BBC/Ayo Bello
Tun daga ranar 25 ga watan Yuli, aka rufe gefe daya na kan gadar, sannan aka bude wa ababen hawa daya gefen, yayin da ake gudanar da wasu muhimman gyare-gyare.

Asalin hoton, BBC/Ayo Bello
Birnin na Lagos a cunkushe yake, sananne ne wajen cunkoson ababan hawa. Ya mamaye tsibirai da dama inda ya nausa har zuwa tsallaken wajen kwaryar birnin, inda nan ne wuri mai sauki na samun wurin zama.

Asalin hoton, BBC/Ayo Bello
A shekarar 1980 ne aka gina gadar ta 'Third Mainland Bridge' kuma tana da tsawon fiye da kilomita 11 (mil 6.8).
Ita ce mafi tsawo kuma mafi cunkoso daga cikin gadojin uku da suka hada kwaryar birnin da kuma tsibiran, yankin da wasu masu hannu da shuni ke zaune.

Asalin hoton, BBC/Ayo Bello
Yayin gudanar da aikin gyaran, an amince wa ababen hawa su rika bi ta gefe daya na gadar ne, daga ƙwaryar birnin zuwa wadannan tsibirai tun daga tsakar dare har ya zuwa tsakar rana.

Asalin hoton, BBC/Ayo Bello
A wadannan sa'oi 12, ababen hawa za su iya wucewa a daura da gefen da ake gudanar aikin, wajen sake dawowa tsakiyar birnin.
Wannan na nufin ma'aikata dama da ke kokarin tunkarar tsibiran don zuwa wuraren ayyukansu.

Asalin hoton, BBC/Ayo Bello
Masu jiran motocin haya na kokawa cewa hakan ya haifar musu da tafiyar hawainiya wajen kai wa ga inda suka dosa.
"Mu kan bar gida da wurwuri amma duk da haka mu kan isa wuraren aiki a makare, hakan bai yi daidai ba,'' in ji Bolaji, wata 'yar kasuwa da ke zaune a tsakiyar birnin ta shaida wa BBC yayin da take jiran motar haya.

Asalin hoton, BBC/Ayo Bello
Kamar sauran mutane, tana hawa motar haya ne don zuwa wurin aiki, amma Bolaji ta ce motocin hayar kadan ne wadanda ke kai-komo kuma akwai tsada sosai.
"Kafin rufe gadar, mu kan yi jiran da bai wuce minti 30 ba kafin zuwan motar safa, amma yanzu mun shafe fiye da awa daya wanda hakan ba yi daidai ba….. [kuma] suna ta kara kudin hawa motar

Asalin hoton, BBC/Ayo Bello
George, wani dan kasuwa, ya bayyana cewa motocin safa-safa sun fi hawa titinan da kuma saukin kudi kafin rufe daya gefen gadar, amma ya ce cunkoson ababan hawa na yamma ya fi ko wanne muni.

Asalin hoton, BBC/Ayo Bello
"Zuwa tsibiran, ba ya daukar lokaci sosai, amma wajen dawowa…. a kan dauki tsawon akalla sa'o'i biyu,'' ya shaida wa BBC.

Asalin hoton, BBC/Ayo Bello
Takawa a kan gadar ba dabara bace saboda tsayinta kuma wasu na fargabar yiwuwar 'yan daba su yi musu fashi.
Wannan matar na dan takawa a kan gadar don zuwa wurin zaman jiran motar haya.

Asalin hoton, BBC/Ayo Bello
An rufe daukacin kan gadar ne har na tsawon kwanaki lokacin bukukuwan Kirsimeti don a zuba kankare, bayan da mahukunta suka ce girgidin da ababan hawa ke haddasawa ka iya hana kankaren kamewa sosai.

Asalin hoton, BBC/Ayo Bello
Ana sa ran sake bude gadar a karshen watan Janairu.
Ana danganta jinkirin ne da zanga-zangar nuna kin jinin cin zali daga rundunar musamman ta 'yan sandan SARS mai lakabin EndSars, da aka gudanar a cikin watan Oktoba a fadin kasar.

Asalin hoton, BBC/Ayo Bello
Duka waɗannan hotunan na da haƙƙin mallaka.










