Kyawawan hotunan shekarar 2020 da masu ɗaukar hoto suka zaɓa

An wallafa

Kafar yada labarai ta PA mai ɗaukar hotuna, ta zaɓi hotunan da suka fi kyau a shekarar da ta gabata tare da bayyana labaransu.

Pete Byrne

"Titunan Llandudno sun yi tsit saboda dokar kullen annobar korona, wanda hakan ya bai wa awaki a Wales damar yawo cikin 'yanci babu takura a cikin birnin.

"Ina tsaka da wani aiki aka kirani a waya daga sashen ɗaukar hoto domin in je in ɗuki hoton waɗannan awaki.

"Bayan share mil 90, wato tafiyar awa biyu a mota, da farko banga komai ba.

"Ban ji daɗi ba lokacin da na yi zaton ba zan same su ba, na yi tunanin sun koma kan dutsen da suke rayuwa.

"Nan da nan na koma baya domin neman wani shago da zan sha gahawa, ina shan wata kwana sai na yi kiciɓis da su a kan titi.

"Wani kallo da ba zan taɓa manta wa da shi ba."

Aaron Chown

"Wani lokaci kenan a watan Maris, yayin da Sarauniya ta fito daga fadar Buckingham domin ziyarar Window Castle, ta samu rakiyar dan karenta.

"Ba kamar yadda aka saba ba, ta bar Landan a hukumance mako guda kafin fara hutun Easter,

Kwanaki hudu kafin a sanya dokar kulle a Burtaniya.

"Har yanzu Sarauniyar ba ta koma fadar Buckingham ba, babu kuma wani bayani game da shirin dawowarta.

"Cikin tsawon shekaru 60 da ta yi kan mulki, wannan ne dogon lokacin da Mai martabar ta dauka ba ta fadar Buckingham ."

Jonathan Brady

"Wani mutum ne ke zaune kusa da lasifika shi kadai a cikin wani lambu, ni kadai ne mai daukar hoton da aka yarda ya shiga wajen.

"haka kuma, ina ganin akwai wani abu tattare da wannan hoto, wanda aka dauka lokacin da ake bukatar wani bayani mai cike da rikitarwa a Burtaniya.

"Wannan hoton da wasu, su ne suka mamaye kusan duka jaridun kasar washe gari.

"Babu shakka lokacin ne da mai bai wa Firaiministan Burtaniya Boris Johnson shawara a bangaren siyasa Dominick Cummings, ya tsaya a cikin wannan lambu da ke lamba 10 a kan titin Dawning domin yin bayani game da tafiyar da yayi lokacin da aka sanya dokar kulle a fadin kasar.

"A fahimtata kasancewa ta mai daukar hoto guda da ya samu shiga wurin na nufin wani babban aiki a wurina.

"Babu wani mai hoto da zai goga kafada da ni, dan haka duk wani abu da na gaza samu zai kasance wani rikicin ne tsakanin mai hoto da tunaninsa.

"Babu abin da muka rasa, bana tunanin mun bar wani abu."

Ben Birchall

" A waje na, wannan hoton ya taƙaita duka fushin da mutanen Burtaniya da kuma na duniya suka yi game da yadda ake yi wa mutane baƙar fata, da kuma fafutukar neman samun 'yanci lokacin da ake fama da guguwar Black Lives Matter.

"Mutum mutmin Edward Colston wani fitaccen mai cinikin bayi a karni na 17, za a iya ganin yadda ake kokarin jefa shi ruwa akan gadar Peros.

"An sanya wa gadar suna Pero Jones, wanda aka kawo Bristol lokacin yana shekarar 12 ya kuma yi aiki a matsayin bawa ya mutu bayan shekarar 32.

"Waɗannan abubuwan biyu a hoton sun haifar da wani tarihi da kumwa wani labari ba kamar sauran labaran hotunan da nadauka ba."

Dominic Lipinski

"Wannan na ɗaya daga ciki hotunan da na ɗauka waɗanda nake ji da su lokacin da aka sanya dokar kulle a fadin kasar a watan Yuli.

"Yadda aka dauki wannan gagarumin hoton na Sarauniya Elizabeth II da ake gani, wata fuska ce a ba a saba gani ba a ko ina."

Jacob King

"A farkon wannan hoto, Margaret Keenan mai shekarar 90 ta sha tafi daga wajen abokan aiki, bayan ta dawo inda take aiki, a zamanta na mutum ta farko a duniya da aka fara yi wa rigakafin korona ta kamfanin Pfizer-BioTecha wajen asibitin Jami'ar Coventry.

"Wannan ya nuna irin mawuyacin halin da aka shiga a lokacin korona, kuma wani lokacin da ake sa ran kawo karshen cutar ga mutane da yawa.

"Na yi matukar dace a matsayin mai hoton da ya halarci taron, kuma yadda hoton ya fito ya samar da kwanciyar hankali a tsakanin kafafen yada labarai da kuma al'umma kan cewa za a iya shawo kan cutar lokacin da ake kokarin shiga 2021."

Danny Lawson

"Hoton shi ne na karshe cikin hotunan da na yi da na dauka a arewacin Ballets bayan dawowa wasa lokacin dokar Covid-19.

""Na shafe kwanaki biyu ina aiki tare da masu rawa lokacin da suke atisaye karkashin dokar korona.

"An dauki hoton ne yayin atisaye na karshe a daren da aka bude gasar."

Brian Lawless

"An dauki wannan hoton a ranar Good Friday lokacin da Ireland ke daf da shiga dokar kulle, lokacin da ake ci gaba da samun masu kamuwa da cutar sai Taoiseach Leo Varadkar ya sanar da kara tsaurara dokar kulle.

"A wajen mutanen Ireland da mafi yawansu mabiya Katolika ne, Good Friday na da mahimmanci musamman da tsofaffi.

"Haka lokacin Easter da ake bukukuwa ake zama tare da mutane a yi murna sai dai wannan karon ba za a yi hakan ba.

"Hoton babu wani abubuwa a cikinsa amma dai na cikin hotunan ma su inganci da na dauka nake so."

Andrew Milligan

"ina wajen rahoton yi wa masu aikin lafiya ta fi a asibitin Sarauniya da ke Glasgow, inda ma'aikatan aikin gaggawa suka saba tsayawa a bakin kofar shin ga sashen ba da kulawa ta musamman suna tafi.

"A daidai wannan lokacin, agogo na kadawa, sai duka ma'aikatan suka juyo wajen suka fara mani tafi, suka ja hankali na kan daidai tagar da ma'aikatan ke sanye da kayan kariya.

"Ma'aikatan uku sun cika tagar yadda ya dace, sanye da kayansu shudaye suna tsaya a waje."

Yui Mok

"Hoton da ya fi kowanne cikin wadanda na dauka a wannan shekarar, na dauke shi ne a ranar 30 ga watan Janairu 2020, Lokacin da aka yi kasa-kasa da tutar daga jikin inda take, a wajen majalisar tarayyar Turai da ke Bruassels a Belgium, domin nuna ficewar Burtaniya daga tarayyar bayan shekarar 47 da ta yi a Kungiyar.

"Ina san hoton saboda abin da yake nunawa kuma da tarihin da yake tattare da shi, hoton ba wai kawai sauke tutar ya ke nuna wa ba, yana kuma kawo karshen rikicin siyasa da matsalar tattalin arziki."

Niall Carson

"Hoton da na fi so a 2020 shi ne na igiyar ruwa wadda ta juya saboda guguwar Hurricane a gabar ruwan Sligo.

"Nasamu labari ne kwana guda kafin nan, da misalign 05:30 wato tafiyar awa hudu a mota daga gida na.

"Na isa wajen da wurwuri domin na samu daukar igiyar ruwa kafin a gama wasan.

"Duka dai, wata dama ce ta minti biyu da ta faru a wani lokacin mai mahimmanci."

Ian West

"Bikin bada lambar girmamawa na Oscar da aka bude cikin dare a Los Angeles, bayan ka gano inda aka tura ka aiki sai ka kare da daukar hotuna na sa'o'i.

"Bayan kwashe kimanin awa takwas kafadunmu sun fara zafi, bayanmu ya yi kamar zai karye, amma dole ne ka tsaya inda kake saboda wadanda za a yi bikin akansu ba su karaso ba.

"Da misalin karfe 01:00 ya yinin Renee Zellweger ta karaso da kyautarta da ta samu.

Mike Egerton

"Daya daga cikin ribar daukar hoton kwallon kasa babu 'yan kallo shi ne ka nuna za ka iya aiki da intanet daga ko ina a cikin filin wasan.

"Kamar yadda aka fara wasan a yammacin, na san kan a kare wasan inuwa za ta mamaye wani bangare na filin wasan.

"Ba hawa saman da na yi zai iya samun damar daukar hoton da inuwar da ba a saba gani ba ta fito a kan ciyawa.

"Ba sauki ba ne da shi samun daukar hoton 'yan wasa uku a wuri daya."

Liam McBurney

"Yadda Kath ta yi da fuskarta ya burgeni lokacin wata ziyarar da ta kai ziyarar bude wata gona a Newtondars a kusa da Belfast.

"Wani murmushi ne mai daukar hankali kuma na gaskiya da ta yi.

"Kuma ina tuna hoton saboda akuyar da suka gani a cikin gonar da ta yi tsalle mai burgewa.

Victoria Jones

"An nemi da in je wani aikin hoto a barikin Wellington da ke Landan saboda sabon karensu.

"Kamar yadda nsojoji ke da yawa, sai kawai aikin ya fara zama sai abin da ake so ka yi sai ya fara ban taba zaton zan samu wani hoto mai kyau ba a wajen.

"Wani kare da bai fi wata shida da haihuwa ba sai ya fara wasa yana damun mutane, to sai mai kula da shi wanda dan kasar Ireland ne sanye da kayan masu ba da kariya ya janye shi daga wajen taron.

Tim Goode

"An dauki wannan hoton ne a gasar zakarun tseren keke ta duniya, da aka yi a watan Fabrairu a birnin Berlin.

"Ginin Velodrom ba wani mai kayatarwa ba ne daga ciki ko waje, dan haka zaka yi ta ƙoƙarin kaucewa abubuwa da yawa kamar su talla da sauransu da ke a mamaye da ginin.

"Ɗaya daga cikin hanyoyin da zaka magance haka sai ka dauki hoto mai juyawa, wanda zai ba ka damar daukar hoton a hankali, ka mai da hankali kan matukin keken, sai ka mayar da komai shudi a wajen banda shi.

All photographs subject to copyright.