Christmas 2020: Kalli hotunan bikin Kirsimeti a duniya

An wallafa

Mutane a sassan duniya daban-daban suna bikin Kirsimeti. Amma a wannan shekarar bikin ba ya armash sosai saboda babu damar mutane su cika coci-coci sakamakon matakan hana yaɗuwar annobar cutar korona da ake yi a duniya. A yanzu sanya takunkumi da bai wa juna tazara ne sabbin abubuwan da dole mutane su bi.

People wear Christmas-themed attire at Bondi Beach in Sydney, Australia. Photo: 25 December 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A Australia, mutane ne sanye da kayan da ke nuna alamar bikin Kirsimeti ke wasanni a bakin tekun Bondi da ke birnin Sydney
Women wearing Santa hats bodyboard on Christmas Day at Tynemouth Beach on the North East coast.

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, A wani gaɓar teku a Ingila ma masu ninƙaya ne ke ɗaga malafarsu tab Kirsimeti don nuna murna
Mary Orme and her son Michael McKimm arrive for a Christmas Day visit with their mother and grandmother, Rose McKimm, at Aspen Hill Village care home in Hunslet, Leeds.

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, A wani yanki na Ingilan dai wata uwa ce da anta suka sanya kayan kariya a yayin da suka kai ziyarar gidan kula da tsofaffi
Pope Francis leads a Christmas Eve Mass at St Peter's Basilica in the Vatican. Photo: 24 December 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Fafaroma Francis ya jagoranci addu'o'in jajiberin Kirsimeti a Cocin St Peter's Basilica a Fadar Vatican tare da mutane ƙalilan
Indonesian Christians wear protective masks and practice social distancing as they pray during the Christmas mass at Immanuel Church amid the COVID-19 pandemic on December 25, 2020 in Jakarta, Indonesia.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Waɗannan Kiristocin a babban birnin Indonesiya wato Jakarta suna addu'o'i ta hanyar bin dokar bai wa juna tazara
A worshipper wearing a plastic visor and face mask prays during Christmas Day Mass at St. Mary's Cathedral on December 25, 2020 in Tokyo, Japan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan ma masu ibadah ne a Tokyo na Japan suke addu'o'i ta hanyar bin matakan kariya
Worshippers of Legio Maria wearing face mask as a preventive measure against the spread of COVID-19 attend the Christmas prayer at their church in the Kibera slum of Nairobi, on December 25, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Kenya masu ibadah sun sanya takunkumi a yayin da suke addu'o'i a wani coci da ke yankin marasa galihu na Kibera
A worker operates a camera for the live broadcast of a Christmas service being streamed online from Yoido Full Gospel Church as measures are taken to protect against the spread of coronavirus (COVID-19) on December 25, 2020 in Seoul, South Korea.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda aka yi addu'o'in Kirsimeti a wani coci da ke Koriya Ta Kudu, sannan an yaɗa shi kai tsaye ta intanet
Children light candles at the entrance gate of the Sacred Heart Cathedral in Delhi, India. Photo: 24 December 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A Indiya kuwa wasu yara ne ke kunna kyandira a gaban kofar shiga Cocin Sacred Heart Cathedral a birnin Delhi
Women wear face masks as they pray during a Christmas Eve Mass in St Andrew's Church in Karachi, Pakistan. Photo: 24 December 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Waɗannan matan suna addu'a a cikin zuciyoyinsu a cocin St Andrew Church a Karachi da ke Pakistan
People gathered around a fire during a Mass in the Virgin Mary Church in Baghdad, Iraq. Photo: 24 December 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A Iraƙi kuwa mutane ne suka taru suka zagaye wuta a yayin addu'o'i a Cocin Virgin Mary da ke Bagadaza babban birnin ƙasar
Employees in a gold shop wear hairbands with reindeer antlers as part of Christmas festivities in the southern Thai province of Narathiwat on December 25, 2020.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Thailand kuwa ma'aikata ne a wani shagon sayar da zinare suke cin nasu bikin a can
A man dressed as Santa Claus greets children at a shopping mall in Jakarta on December 25, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan kuma wasu yara ne a Indonesiya suke sanye da takunkumi a yayin da suke mu'amala da wani mutu da ke sanye da kayan Fada Kirsimas

Dukkan hotunan suna da haƙƙn mallaka