Shinkafa na cikin kayayyakin da Najeriya ta haramta shiga da su ta kan iyaka

An wallafa

Gwamnatin Najeriya ta ce duk da buɗe iyakokinta na tudu da ta yi, har yanzu ba a ɗage dokar da ta haramta shigo da wasu kayayyaki ba da suka haɗa har da shinkafa da motoci a ƙasar.

A ranar Alhamis ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin buɗe wasu iyakokin ƙasar hudu, wadanda suka shafe fiye da shekara ɗaya a rufe.

Iyakokin da gwamnati ta buɗe sun hada da ta Seme da Mfun da Ileleh da kuma Maigatari.

Matakin buɗe kan iyakokin ya faranta ran ƴan Najeriya musamman da fatan cewa harka za ta buɗe, da kuma samun sa'ida daga tsadar rayuwar da ake fama da ita, musaman ma yadda farashin kayan masarufi ke hauhawa.

Sai dai Mista Joseph Attah kakakin hukumar kwastam ta Najeriya ya shaida wa BBC cewa dokar hana shigo da wasu kayayyaki da suka ƙunshi har da na abinci tana nan ba ta kau ba.

Hukumar kwastam ta Najeriya a shafinta na intanet ta zayyana kayayyakin da gwamnatin Najeriya ba ta yadda a shigo da su ba.

  • An hana shigo da shinkafa da taliya da man girki
  • An hana shigo da kajin Turawa ko talo-talo da ƙwai da nama
  • An hana shigo da sukari
  • An hana shigo da tumaturin gwangwani
  • An hana shigo da suminti
  • An hana shigo da sabulun wanka da na wanki da omo
  • An hana shigo da lemon kwali ko na kwalba da ruwan roba (amma bai shafi masu ƙara kuzari ba irin Power Horse)
  • An hana shigo da magunguna da suka ƙunshi Paracetamol da Aspirin da sauransu
  • An hana shigo da maganin sauro
  • An hana shigo da katin waya (recharge card)
  • An hana shigo da dardumar ɗaki
  • An hana shigo da iya kwandishan (Ac) da aka yi amfani da shi da kuma firji
  • An hana shigo da motoci da aka ƙera fiye da shekara 15.

Akwai kuma wasu jerin abubuwa da dama da gwamnatin ta haramta shigo da su a ƙasar kamar yadda hukumar kwastam ta bayyana a shafinta na intanet.

Mista Attah ya ce buɗe boda da aka yi ba wai an ce kowa ya kawo duk abin da yake so ba ne.

Ya ce yanzu wannan matakin da buɗe wasu daga cikin iyakokin zai ba ƙasashen da ke makwabta da Najeriya damar yin harakokinsu na boda yadda doka ta ce.

"Dole su tabbatar da duk abin da ba mu so ka da ya shigo gidanmu kamar yadda ba za su mu bari wani abin da ba su so ya shiga gidansu," in ji shi.

Tun a watan Agustan bara gwamnatin Najeriya ta rufe iyakokinta da ke kan tudu, da nufin inganta tsaro da bunƙasa masana'antun cikin gida. Amma wasu na ganin cewa kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Wasu ƴan Najeriyar na da ra'ayin cewa babu wata ribar a zo a gani da aka samu daga rufe iyakokin ƙasar da gwamnati ta yi, suna kafa hujja da cewa farashin kayan abinci bai faɗi ba, kuma matsalar tsaro sai ƙara ta'azzara take.

Ko da yake hukumar kwastan a nata bangaren ta ce an samu nasara ta bangaren diflomasiyya da kasashe makwabta, saboda rashin fahimtar da aka yi fama da ita a baya, yanzu ta kau.