Isra'ila da Moroko za su mayar da dangantakar diflomasiyya

An wallafa

Moroko ta zama ƙasar Larabawa ta baya-bayan nan da ta amince ta mayar da dangantakar diflomasiyya da Isra'ila a ƙarkashin wani shiri da Amurka ta jagoranta.

A ƙarkashin shirin, Amurka za ta amince Moroko ce ke da iko kan yankin Kudancin Sahara wanda aka dade ana takaddama a kai.

Yankin na Yammacin Sahara ɓangarori biyu ne - Moroco da Polisario Front - ke ikirarin mallakinsa.

Kungiyar Polisario Front ta daɗe tana neman kafa ƙasa mai cin gashin kanta a yankin.

Moroko ce kasa ta huɗu da ta mayar da dangantaka da Isra'ila tun watan Agusta.

Amurkar ta jagoranci irin waɗannan yarjeniyoyin tsakanin Isra'ila da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da kuma Sudan.

Ban da Masar da Jordan, Moroko ce kasar Larabawa ta shida da ta mayar da dangantaka da Isra'ila.

Me yarjejeniyar ta ƙunsa?

Shugaban Amurka Donald Trump ne ya sanar da kulla yarjejeniyar ranar Alhamis a Tuwita.

Fadar White House ta ce Mista Trump da Sarki Mohammed na VI sun amince "Moroko za ta mayar da dangantaka da Isra'ila domin fadada harkar ciniki da kasuwanci da kuma ɓangaren al'adun gargajiya tsakaninsu domin inganta zaman lafiya a yankin."