NANS: An yi musayar wuta a Abuja yayin zaɓen ƙungiyar ɗalibai ta Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

An yi musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da wasu da ake zargin 'yan ƙungiyar ɗaliban Najeriya ne a dandalin Old Parade Ground da ke unguwar Garki a Abuja babban birnin Najeriya.

Lamarin ya faru ne yayin da ake gudanar da babban taron ƙungiyar domin zaben sabbin shugabanni da za su jagoranci ƙungiyar.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter, ya nuna yadda mutane ke guduwa yayin da ake harbe-harben bindiga ba ƙaƙƙautawa. An kuma bayyana cewa wannan ba sabon lamari ne, domin an sha samun irin wannan lamari na harbe-harben bindiga yayin da ƙungiyar ke taronta.

Wani ɗalibi da ya shaida lamarin ya shaida wa BBC cewa ana samun rikici irin wannan ko a baya sakamakon yadda ake tara ɗalibai daga jihohi da dama masu halayya daban-daban.

A cewarsa, an fara rikicin ne bayan an gama tantance waɗanda za su yi zaɓen sai rikici ya ɓarke, inda aka yi ta musayar wuta, amma daga baya komai ya dawo daidai kuma an gudanar da zaɓen.

Mun tuntuɓi 'yan sanda reshen Abuja babban birnin ƙasar domin jin ta bakinsu, amma ba mu same su.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta samu nasarar kama wasu da ake zargi da tayar da tarzomar, haka kuma akwai rahotannin da ke cewa wasu da dama sun samu raunuka yayin artabun.

Kakakin rundunar 'yan sandan ciki ta DSS, ya shaida wa BBC cewa bai da tabbacin labarin an kama mutane da ake zargi, amma ya ce idan har lallai an kama wasu masu nasaba da tashin hankali, to ba zai kasance abin mamaki ba.

Wanda aka zaɓa a matsayin sabon shugaban ɗaliban Najeriya, Sunday Asefon mai shekara 43, ɗan salin jihar Ekiti ne, kuma shi zai ci gaba da jan ragamar ƙungiyar a halin yanzu.

Wannan musayar wutar na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar malamai masu koyarwa ta jami'o'i wato ASUU ke ci gaba da gudanar da yajin aiki, inda ƙungiyar ke ta neman gwamnati ta biya musu wasu buƙatunsu.

Me mutane ke cewa?

Tun bayan da aka yi wannan rikici, muhawara ta ɓarke a shafin Twitter inda da dama ke Allah-wadai da abin da ya faru.

Wannan cewa ya yi, ya kamata a ce wannan taro ne na ɗalibai, amma a cewarsa, lamarin bai yi daɗi ba.

Ya bayyana cewa ta ya za a samu rayuwa mai kyau a nan gaba idan zaɓen ɗalibai yana kama da na PDP da APC?

Wannan kuma yana zargin cewa ƙungiyar ɗaliban ba tana kare muradin ɗaliban ƙasar bane, ya kuma yi zargin cewa kashi 90 cikin 100 na masu takara ba ɗalibai ba ne.

Sharhi

An dade ana samun hargitsi irin wannan a lokutan zabukan kungiyoyin dalibai a Najeriya.

Babban abun da ke kawo rabuwar kai da rikici a lokutan zaben sun hada da samun rarrabuwar kawuna tsakanin bangaren da gwamnati ke goyon baya don kare muradunta da bangaren masu kare muradun kungiyar kwadago da kuma bangaren da ke kare muradun dalibai.

Yawanci a kan samu wadanda sun ma dade da barin duniyar dalibta a jami'o'i amma za a ga suna tsayawa takarar a zabukan kungiyin dalibai, yawancin su sun fara manyanta.

Ba wani abu ke jawo haka ba illa zargin da ake cewa gwamnati ce ke daukarsu haya don su tsaya tsayin daka a zaben du zama masu kare muradunta a lokacin da bukatar hakan ta taso.

Amma abu mafi ban tsoro shi ne ganin yadda matasan da ake sa ran za su gane martabar kasarsu har su karbi shugabancinta wata rana, a irin wadannan lokuta su ne kuma suke juyewa suna zama masu daukar makamai tare da kawo hargitsi tun a kananan zabuka irin na makaranta.