Bidiyo: Labarin matuƙin jirgin saman da ya koma tela a Kano

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Ishaq Ibrahim na ɗaya daga cikin gomman matasan da gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta tura ƙasashen waje don karatun digiri a wasu ɓangarori da suka haɗa da na koyon tukin jirgin sama, a lokacin mulkin Gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso.

Sai dai matashin mai shekara 35 da sauran abokan karatunsa da suka tafi ba su samu damar cimma burinsu na tuƙa jirgi a sararin samaniya ba, saboda wasu dalilai da suka rusa mafarkin nasa.

Amma a yanzu a ƙalla ya tsira da sana'ar ɗinki don rufa wa kansa asiri a birnin Kano.

Ku kalli bidiyon don jin yadda wannan buri nasa ya rushe.