Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
NYSC batch B 2020: Sharuɗɗan da za a cika kafin masu yi wa ƙasa hidima su shiga sansanin horaswa
Kwamitin shugaban kasa da ke yaki da cutar korona da kuma hukumar da ke dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya sun ce dole ne a yi wa masu yi wa kasa hidima na National Youth Service Corp gwajin cutar korona idan suka isa sansanonin horaswa.
A cewarsu, masu yi wa kasa hidimar da suka tafi da sakamakon da ke nuna ba sa dauke da cutar ne kawai za a bari su shiga sansanoni inda za su yi rijista.
Wannan na cikin sharudan da hukumar NYSC, da Kwamitin shugaban kasa da ke yaki da cutar korona da kuma hukumar da ke dakile cutuka masu yaduwa ta NCDC suka gindaya kafin a bar masu yi wa kasa hidima a shekarar 2020 su shiga sansanoninsu a duka fadin Najeriya, wanda ake somawa ranar 10 ga watan Nuwamba, 2020.
Kazalika Shugaba Muhammadu Buhari ya umarni hukumar NYSC ta tabbatar dukkan masu yi wa kasa hidima sun yi rijista da hukumar inshorar lafiya ta kasa.
Shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim wanda ya bayyana hakan, ya kara da cewa suna hada gwiwa da jami'an tsaro domin su tabbatar da tsaron masu yi wa kasa hidima a sansanoninsu da ke fadin kasar.
Wasu rahotanni na cewa za a yi wa masu yi wa kasar hidima gwajin cutar korona ba tare da sun bayar da ko sisi ba suna masu cewa tuni jami'an hukumar NCDC suka bazama cikin sansanonin masu yi wa kasa hidima domin yi musu gwajin cutar.
Sauran sharudan da aka gindaya wajen tabbatar da tsafta a sansanoni su ne:
- Za a samu karin sansanonin masu yi wa kasa hidima a jihohi domin rage cakuduwar jama'a. Hakan zai tabbatar da bai wa juna tazara
- Za a tsaftace dukkan sansanonin masu yi wa kasa hidima kafin a bude su
- Dole a gwada zafin jikin duk mutumin da zai shiga sansanin
- Dole ne masu shiga sansanonin su sanya takunkumi
- Za a sanya tazarar mita biyu tsakanin gado da gado a dakunan da masu yi wa kasa hidima za su rika kwana
- Dukkan masu yi wa kasa hidima za su yi gwajin korona kafin su karbi takardar shiga sansani