Abin da ya sa na koma karatu bayan na yi ritaya - Dattijo mai shekara 70
Wani dattijo mai shekara 71 ya samu nasarar kammala digirinsa na biyu shekara 40 bayan kammala na farko.
Alhaji Shehu EL-Yakub ya yi digirin nasa na biyu ne a kan nazarin zaman lafiya da warware rikice-rikice a Jami'ar Karatu daga gida ta Najeriya, NOUN.
A makon jiya ne dattijon ya miƙa wa jami'ar kundin bincikensa bayan shafe shekara daya da rabi yana karatun.
Alhaji Shehu ya ce ya yanke shewarar komawa makaranta ne bayan ya yi ritaya saboda yana da ragowar ƙarfi a jikinsa, kuma ba ya so ya zauna a gida ba ya komai, kasancewar ya saba da kazar-kazar lokacin da yake aikin gwamnati.
Ya yi aiki a Ma'aikatar Kudi ta Jihar Kano sannan ya koma Babban Bankin Najeriya CBN, inda ya yi ritaya a can bayan shekara 20 a bankin.
Ya shaida wa BBC cewa ba ya yi karatun ne domin ya samu aiki ba.
"A gaskiya Fisabilillahi ba abin da nake nema. Ba na neman a naɗa ni wani muƙami ma ballantana aiki."
Ya ce ya yi digiri na biyun ne kan zaman lafiya da warware rikice-rikice kasancewar ana fuskantar matsaloli da dama a zamantakewar al'umma a matakin unguwanni sa jihohi da kuma kasa baki daya.
Dattijon ya ce a lokacin karatun nasa ya rika zuwa dakin karatu yana bincike, sannan a wasu lokutan yakan shiga intanet don neman karin bayani.
"Hakan ya sa ma'aikatan jami'ar ta NOUN da dalibai suke mamakina, to amma na shaida musu cewa ina jin dadin hakan, kuma na saba da haka tun lokacin da na yi digirina na farko," a cewar Alhaji Shehu.
Dangane da dangantakarsa da malamai kuwa ya ce suna matuƙar girmama shi.













