Muslim Pro: Da gaske ana leƙen asirin Musulmin da ke amfani da manhajar?

Asalin hoton, Twitter/@ajplus
Rahoton da jaridar nan da ke wallafa labarai kan harkokin fasaha ta Vice's Motherboard ta bankado cewa masu manhajar Muslim Pro suna sayar da bayanan Musulmi ga hukumomin leken asirin Amurka ya bar baya da kura.
Muslim Pro manhaja ce da ke dauke da Al Ƙur'ani, wadda kuma mutum fiye da miliyan 98 ke amfani da ita wajen sanin Al-kibla a lokutan sallah da wasu harkoki na addinin Musulunci.
"Rundunar sojin Amurka tana sayen bayanai kan kai-komon mutanen da ke amfani da wannan manhaja a fadin duniya," a cewar jaridar.
Ta kara da cewa rundunar tana sayen manhajoji na dandalin neman aure na Musulmai, da manhajar da ke bibiyar yadda ake tsawa gabanin ruwan sama da kuma manhajar da ke taimakawa wajen shirya dakin barci.
Jaridar, wadda ta bayyana haka a rahoton da ta wallafa ranar Litinin, ta kara da cewa rundunar sojin Amurka ta yi amfani da hanya biyu daban-daban wajen samun bayanai kan wuraren da masu amfani da manhajar ta Muslim Pro.
Rahotanni sun ce rundunar sojin ta Amurka na bi ta hannun kamfanin X-Mode wajen sayen bayanan Musulmin da ke amfani da manhajar ta Muslim Pro.
Wannan labari ya ja hankalin miliyoyin Musulmi a fadin duniya, wadanda ke nuna matukar bacin ransu game da yadda Amurka ke bin diddiginsu.

Sai dai wasu fitattun Malaman addinin Musulci irin su Yasir Qadhi sun ce ba su yi mamakin wannan kutse da rundunar sojin Amurka ke yi wa Musulmi ba.
A sakon da ya wallafa a hafinsa na Facebook ya ce: "Ko da yake ya wajaba su yi bayani kan abin da suka yi, amma shin wannan ya bai wa kowa mamaki? Kamar yadda Edward Snowden ya nuna, dukkan bayanan intanet marasa tsaro, musamman a Gmail da Google, hukumar leken asirin Amurka na sanya musu ido."
Sai dai ya ce ba ya so hakan ya zama wata hanyar karfafa gwiwar Musulmi su rika leken asiri ko bin diddigin mutane.
Ita kuwa Vanessa Taylor cewa ta yi labarin da ya nuna cewa Muslim Pro na sayar da bayanai ga sojojin Amurka "wata tunatarwa ce da ke nuna irin yaudarar da ke cikin leken asiri."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
A nasa bangaren, Abdullah Ayaz Mullanee, ya yi kira ga masu amfani da manhajar su goge ta daga cikin wayoyinsu sannan su watsa labarin domin wasu su dauki irin wannan mataki.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Yadda za ku kare kanku daga kutse
Masana harkokin sadarwa sun ce da ma can masu amfani da manhajojin da suka sauke a intanet ba sa samun tsaro dari bisa dari.
Abdullahi Salihu Abubakar - wanda aka fi sani da Baban Sadiq - wani masanin fasahar sadarwa ne a Abuja, kuma ya shaida wa BBC cewa "sanin sirrin masu amfani da manhajoji a intanet ya zama ruwan dare domin kuwa ba a kare bayanan sirri dari bisa dari a intanet."
Sai dai ya ce abin bakin ciki shi ne yadda masu irin wadannan manhajoji suke sayar da bayanan mutane ga hukumomin tsaro da 'yan kasuwa da sauran irin su da ke sanya ido kan mutane.
Ya kara da cewa ko da yake galibin wayoyin salula ba su da sirri amma "wayar Android ta fi rauni wajen tabbatar da tsaro domin kuwa ana sanin duk abin da mai amfani da ita yake ciki."
Baban Sadiq ya bayyana cewa "yana da kyau mutane su rika duba setting da ke wayoyinsu, su gyara abubuwan da suke so da wanda ba sa so a sani game da su."










