An kama yaron da ya saci rigar sajan na 'yan sanda a lokacin zanga-zanga

.

Asalin hoton, Other

An wallafa

'Yan sanda a jihar Edo da ke kudancin Najeriya sun kama wani yaro mai shekara 11 bayan an kama shi sanye da kayan sarki na sajan ɗin 'yan sanda da ya sata.

Bayanai sun bayyana cewa yaron ya shiga zugar 'yan dabar suka kai wa wani ofishin 'yan sanda hari yayin zanga-zangar EndSars a jihar Edo.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Edo, SP Chidi Nwabuzor, ya shaida wa BBC cewa yaron mai shekara 11 na daga cikin 'yan daban da suka fasa wani wurin ajiyar kayayyaki inda suka tafka sata, kuma an kama yaron yana sanye da kayan 'yan sanda a lokaci da aka kama shi.

.

Asalin hoton, Edo state police command

Wasu kafafen watsa labarai na Najeriya sun ruwaito cewa yaron na daga cikin waɗanda suka kai hari a ofishin 'yan sanda na Oba Market, inda bayan harin ne ya saka kayan 'yan sandan kuma ya ayyana kansa a matsayin babban sufeton 'yan sanda.

Hoton wannan yaron sanye da kayan 'yan sanda ya cika kafafen sada zumunta amma Mista Nwabuzor ya bayyana cewa rundunar 'yan sandan reshen jihar Edo ba ta tasa ƙeyar yaron ba tare da sauran 'yan daban da aka kama ba a ranar Lahadi saboda ƙarancin shekarunsa.

"Kun san cewa ba a yi wa ƙaramin yaro shari'a, (sai wanda ya kai shekara 18), haka lamarin yake kan batun tasa ƙeyar da 'yan sanda ke yi, ba mu tasa ƙeyar wanda bai kai 18 ba," in ji shi.

.

Asalin hoton, Edo state police command

Mai magana da yawun 'yan sandan ya bayyana cewa za su miƙa yaron mai shekara 11 ga wurin horar da yara, wanda shi ne daidai wurin da ya kamata a kai wanda bai kai shekarun da za a yi shari'a da shi ba.

A kwanakin baya ne dai zanga-zangar EndSars ta bar baya da ƙura bayan 'yan daba sun ƙwace ragamar zanga-zangar inda suka koma kai hare-hare ofisoshin 'yan sanda da kamfanoni da kuma fasa wuraren ajiyar kayayyaki musamman na abinci.

'Yan sanda a jihar ta Edo sun bayyana cewa 'yan dabar sun ƙona ofisoshin 'yan sanda da dama tare da satar makamai da harsasai da kuma yi wa wasu mata fyaɗe, a wasu wuraren kuma har da kashe 'yan sandan, da kuma sakin fursunoni da fasa shaguna.

Ko a ranar Juma'a sai da Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya bayyana cewa an kashe 'yan sanda 22 a Najeriya tare da lalata ofisoshin 'yan sandan 205 a fadin ƙasar.