Saudiyya ta buɗe Ka'abah ga dukkan masallata daga Lahadi

Asalin hoton, HARAMAIN SHARIFAIN
Hukumomin Saudiyya sun sanar da sake bude masallacin Al-Haram na Ka'abah - wuri mafi tsarki da daraja ga musulmi bayan an rufe shi na wata bakwai.
Kafofin watsa labarai na Saudiyya, kamar tashar talabijin ta Saudi Television da shafin Tiwita na Haramain Sharafain, sun ruwaito cewa an kyale 'yan kasar har da mazauna birnin Makkah shiga harabar masallacin Ka'abah domin yin salloli biyar na farali da ma sauran ibadu.
An dai rufe masallacin ne saboda annobar korona wadda har ta shafi ayyukan ibada kamar aikin Hajji da na Umrah.
Shafin Tiwita na Haramain Sharifain ya wallafa wani takaitaccen bayani, wanda a ciki yake sanar da duniya cewa:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
"Nan da sa'o'i kalilan... za a bude kofofin Masjid al Haram ga kowa domin gabatar da ibadun khamsat salawat bayan hanin da aka yi na wata bakwai." Sai dai sanarwar ta ce akwai sharuddan da ake bkatar masu shiga masallacin su tabbatar sun cika gabanin shiga harabar masallacin. Wannan ya hada da sanya takunkumi.
A wani labarin mai alaka da wannan, Saudiyya ta sanar da mutum 250,000 ne za a bari su gudanar da aikin umrah daga yau 18 ga watan Oktoba.
Wannan ne kashi na biyu na shirin mayar da al'amuran ibadu kamr umrah da aikin hajji yadda aka san su a baya tun bayan da aka takaita lamurra saboda bayyanar annobar korona.
Za a kuma kyale massallata su ziyarci wurare masu daraja kamar Rawdah Sharif da yankin tsohon masallacin Annabi a Madinah daga yau.
Masu bukatar shiga masallatai biyu mafi tsarki da ke Makkah da Madinah za su rika yin rajista ne ta hanyar amfani da wata manhaja ta musamman mai suna Eatmarna App wanda zai ba su damar yin umrah da kuma shiga Rawdah Sharif.
Maniyyata daga ƙasashen waje ma ba a bar su a baya ba, domin daga ranar 1 ga watan Nuwamba za a kyale maniyyata daga dukkan kasashen duniya su fara gudanar da Umrah har ma da ziyartar Rawdah Sharif - wanda shi ne mataki na uku cikin shirin mayar da al'amuran ibada yadda aka san su a ƙasar ta Saudiyya.











