An bai wa wasu mata kyautar Nobel don bajintarsu ta ƙirƙirar fasahar jirkita ƙwayoyin halittun gado

An wallafa

An bayar da kyautar Nobel ta bana a ɓangaren ilimin sinadarai ga wasu mata biyu saboda bajintarsu ta ƙirƙirar wata fasahar jirkita ƙwayoyin halittun gado.

Emmanuelle Charpentier daga Faransa, da takwararta Ba'amurkiya, Jennifer Doudna, su ne mata na farko da aka bai wa kyautar ba tare da wani namiji ba a kirkirar tasu.

Aikinsu ya bai wa masana kimiyya damar cire wa wata ƙwayar halittar gado a jikin wani abu mai rai.

Tuni aka fara amfani da fasahar wajen haɓaka amfanin gona da za su iya jurewa ƙwari da fari kuma tana ba da gudummawa ga sabbin hanyoyin warkar da cutar daji.

Fasahar cike take da taƙaddama, wasu na sukar fasahar wadda a ganinsu na kawo sauyi ne ga rayuwa.

An bai wa wasu mutum uku kyautar Nobel kan gano Baƙin Ramin sararin samaniya

A hannu guda kuma an bai wa wasu masana kimiyya kyautar karramawa ta Nobel a fannin kimiyyar Fiziks don ƙoƙarinsu na gano baƙin rami na ''black hole.''

An bayyana sunayen Roger Penrose da Reinhard Genzel da Andrea Ghez waɗanda suka yi nasarar ne a wani taron manema labarai a Stockholm.

Mutanen za su raba kuɗin fam miliyan 864,200 a tsakanin su.

David Haviland, shugaban kwamitin ba da kyaututtukan na fannin fiziks, ya ce kyautar ta bana ta karrama ɗaya daga cikin wasu abubuwa na ban mamaki ne da aka gano a duniya.''

Baƙin rami yankuna ne a sararin samaniya da suke da maganaɗisunsu ke da ƙarfi ta yadda ko haske ba zai iya giftawa ta wajensu ba.