Hotunan shirye-shiryen buɗe Masallacin Ka'aba ga masu Umara

An wallafa

Ga wasu zaɓaɓɓun hotuna na yadda ake shirye-shiryen buɗe Masallacin Ka'aba ga masu Umara, wanda shafin Haramain suka wallafa a Tuwita.

Saudiyya

Asalin hoton, Haramain

Bayanan hoto, A ranar Laraba ne shugabannin Masallatan Biyu Masu Daraja suka tattauna kan shirin tabbatar da cewa maniyyata sun isa lafiya a yayin da suka je da niyyar Umara.
Saudiyya

Asalin hoton, Haramain

Bayanan hoto, A ranar 23 ga watan Satumba ne mahukunta a Saudiyya suka sanar cewa za a kyale mazauna ƙasar su gudanar da ayyukan ibada na Umara bayan ta dakatar da ita na tsawon watanni.
Saudiyya

Asalin hoton, Haramain

Bayanan hoto, Hukumomin ƙasar sun ce daga baya za su kyale maniyyata daga ƙasashen waje su shiga ƙasar domin gudanar da ibadar wadda take da muhimmanci ga Musulmin duniya.
Saudiyya

Asalin hoton, Haramain

Bayanan hoto, Sai dai za ta ƙayyade yawan maniyyatan da yawan ƙasashen da za ta bari su shiga ƙasar.
Saudiyya

Asalin hoton, Haramain

Bayanan hoto, Maniyatta da ke cikin Saudiyya na iya yin Umrah daga ranar 4 ga watan Oktoba, inda maniyattan da ke ƙasashen ƙetare kuwa sai sun jira zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba kafin su sami izinin shiga ƙasar.
Saudiyya

Asalin hoton, Haramain

Bayanan hoto, Masu aikin tsaftace Masallacin Ka'aba ne ke bakin aikinsu a nan. Suna ta kula da yadda abubuwa ke gudana.
Saudiyya

Asalin hoton, Haramain

Bayanan hoto, Sheikh Abdurrahman Sudais ne shugaban Masallatan biyu masu daraja na Makkah da Madina, kuma ƙarƙashin jagorancinsa ake aiwatar da komai