Iyalan sojan da aka yanke wa hukuncin ɗauri kan kisan kai sun ƙwace shi a kotu a Chadi

File image of the Chadian capital, N'Djamena

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lamarin ya faru ne a babban birnin Chadi N'Djamena
An wallafa

An tayar da hargitisi a wata kotu a Chadi lokacin da wasu iyalan wani soja da aka yanke wa hukunci kan kama shi da laifin kisa suka ƙwace shi tare da ɓatar da shi daga cikin kotun.

An yanke wa Kanal Abdoulaye Ahmat Haroun hukuncin ɗaurin shekara biyar ne kan laifin kisan kan da ya jawo ce-ce-ku-ce a ƙasar.

Jim kaɗan bayan hakan ne, wasu danginsa har da masu ɗauke da makamai suka dirar wa kotun tare da fitar da shi daga cikinta.

Sai dai ƴancin da ya samu na ƙwace shi da danginsa suka yi bai yi nisan zango ba. Ministan Shari'a Djimet Arabi ya ce sa'a biyar kacal bayan hakan aka sake kamo Haroun.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a birnin N'Djamena, babban birnin ƙasar Chadi.

An tuhumi Haroun da laifin kisan kai bayan da wani bidiyo ya yaɗu a intanet da ke nuna shi yana nuna wa mutum biyu bakin bindiga a watan Agusta, inda ya kashe ɗaya daga cikinsu.

Bidiyon ya jawo muhawara a shafukan sada zumunta, inda wasu ke cewa Haroun ɗan ƙabilar shugaban ƙasar ne Idriss Deby Itno, wanda ya shafe shekara 30 yana mulkin Chadin. Wasu sun ce sojan ya aikata hakan ne don yana ganin ''ya fi ƙarfin hukunci.''

map locator

Muhawarar da ake yi a shafukan sada zumuna ta yi zafi ta yadda har gwamnati ta yanke ƙarfin intanet don hana yaɗuwar saƙonni.

Shugaban hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta Chadi Maxvelt Loalngar, ya ce dangin kanal ɗin da wasun su ke riƙe da ''makaman soji'' sun fitar da shi daga kotun, suna kiran alƙalin ''bawa'' a yayin da suke ficewa.

Ministan Shari'a Arabi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ''matasa da mata ne suka fara faɗan ƙarya'' don taimaka wa wajen fitar da shi ɗin.

Ya ƙara da cewa a ƙarshe ƴan sanda sun kamo kanal ɗin sojan da wasu mutum biyar a wani gida da suka ɓuya'.

Wannan ne karo na biyu da Haroun ya yi ƙoƙarin gujewa shari'a.

A ranar 9 ga watan Agusta a lokacin da yake tsare, ya yi ƙoƙarin guduwa Masar a wani jirgi. Masu shigar da ƙara sun bai wa jirgin umarnin koma wa N'Djamena, inda aka kama shi bayan saukar jirgin.