'Yan Kannywood na murna kan sinimar da El-Rufai zai gina musu

Asalin hoton, Falalu Dorayi
Masu ruwa da tsaki a masana'antar Kannywood sun cika da murna sakamakon matakin da gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya dauka na ba su fili da kuma kudin da za su aza ginin sinima a jihar.
Gwamnan ya ba su fili mai fadin murabba'i dubu 8000 domin gina babbar sinima ta zamani, da kuma gudunmawar kudin na fara aza harsashi, a cewar wani fitaccen tauraro kuma furodusa na Kannywood, Malam Falalu Dorayi.
A cewarsa, masu ruwa da tsaki na Kannywood karkasin wata kungiya da ake kira Movie Hope ne suka nemi gwamna ya ba su filin da za su gina katafariyar sinima wadda a cikinta za a iya daukar fina-finai sannan a nuna su.
"Da ma an dade da kai masa kuka cewa akwai bukatar a samu fili a Kaduna wanda za a gina sinima, kamar yadda aka bukaci wasu gwamnoni su ma su yi a jihohinsu. Ginin zai kunshi sinima da wurin koyon sana'o'i da wurin yin daukar muryar mawaka da kuma sutudiyo, da wuraren cin abinci da wuraren shakatawa," in ji Falalu Dorayi.
Ya ce a makon nan ne kungiyar tasu ta samu jagorancin Musa Halilu (Dujiman Adamawa) inda suka ziyarci Gwamna El-Rufai wanda ya cika musu alkawarin ba su fili da kuma wani bangare na kudin gina sinimar.
Fitattun taurari maza da mata - na da da na yanzu - ne suka je yi wa gwamnan na Kaduna godiya.
Cikinsu akwai Ibrahim Mandawari, Saratu Gidado(Daso), Hadizan Saima, Rabi'u Rikadawa, Maryam Yahaya, Musa Mai Sana'a, Bello Muhammad Bello, da dai sauransu.
Ƙishirwar sinima da katafaren dandalin yin fim
Masu ruwa da tsaki a masana'antar Kannywood sun dade suna kishirwar wuraren da za su rika shirya fina-finai da kuma sinimomin da za a rika nuna su.
A shekarar 2016 ne gwamnatin tarayyar kasar ta so gina katafaren dandalin yin fim a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
A wancan lokacin, masu harkar fina-finai sun yi maraba da matakin, inda suka bayyana shi da cewa wata hanya ce da za ta bunkasa harkar fina-finai a Najeriya da samar wa dubban mutane ayyukan yi.
Sai dai masu adawa da wannan mataki sun yi ta sukansa suna mai cewa zai ruguza tarbiyyar al'umma, wadanda da ma wasun su ba sa ga-maciji da masu harkar fina-finai.
Daga bisani gwamnati ta dakatar da shirin lamarin da ya yi matukar bata ran 'yan Kannywood.

Asalin hoton, Instagram/@nuhuabdullahi

Asalin hoton, Falalu Dorayi

Asalin hoton, Falalu Dorayi











