Ali Nuhu: Me ya sa aka naɗa jarumin a matsayin jakadan La Liga a Arewa?

Asalin hoton, Arewa Radio
An naɗa fitaccen jarumin fina-finan Hausa na Kannywood Ali Nuhu a matsayin jakadan La Liga a Arewacin Najeriya.
An yi naɗin ne a wani taro da La Liga da kuma rediyon Arewa suka shirya a jihar Kano da ke arewa maso yammacin kasar.
A cewar Sheriff Abdallah wanda ya shriya taron, Kano ita ce gidan gasar La Liga sannan shirin wanda shi ne irinsa na farko mafari ne na zuwan wasu abubuwan ci gaba a Najeriya da ma Arewacin ƙasar.
"Mun kusanto da La Liga kusa da magoya baya, yanzu aka soma kakar wasannin kuma ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba saboda za mu ci gaba da inganta alaƙa tsakanin (La Liga) da kuma magoya bayansu a Najeriya," a cewar Abdallah.
Shi ma tsohon ɗan wasan Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Super Eagles kuma jakadan La Liga a Najeriya, Mutiu Adepoju ya bayyana jin daɗinsa kan yadda ake samun dumbin magoya bayan gasar a Kano da sauran wasu yankunan Arewacin Najeriya.
Tsohon ɗan wasan ya buƙaci masu kallon gasar da su ci gaba da karfafa haɗin kai a tsakaninsu duk da banbancin ra'ayi da suke da shi a ƙwallon ƙafa.

Asalin hoton, Arewa Radio
Sabon jakadan, Ali Nuhu ya shaida wa BBC cewa La Liga ta shirya taron kasancewar akasarin magoya bayanta a yankin Arewacin Najeriya suke kuma Hausa ce harshen da aka fi amfani da shi a yankin.
Kuma a cewarsa, kasancewar harshen Hausa na da faɗi, La Liga na son ta zama kusa da magoya bayanta da ke Najeriya musamman a Arewacin ƙasar.
Ya ce hakan zai sa magoya baya su san cewa La Liga na tare da su.
Wannan muƙamin wata dama ce ta zama jigo tsakanin magoya baya da La Liga, in ji Ali Nuhu.
A yanzu haka Ali Nuhu ya ce yana shirin tafiya kasar Spaniya domin kallon wasa biyu na La Liga, da zarar an ci gaba da zirga-zirga tsakanin Najeriya da Spaniya.
Alfanun naɗin
A cewar fitaccen jarumin akwai alfanu da dama da ke tattare da naɗin nasa a matsayin jakadan La Liga a yankin Arewacin Najeriya kuma sun haɗa da:
- Magoya baya za su san cewa La Liga ta san da su.
- Gudanar da taruka akai-akai don ƙara kusanci tsakanin magoya bayan La Liga.
- Shirya gasa tsakanin magoya bayan kulob-kulob na La Liga.











