Juyin mulki a Mali: An tashi baram-baram kan batun kafa gwamnatin riƙo

Asalin hoton, Getty Images
An kammala taro tsakanin Sojoji da sauran masu ruwa da tsaki kan batun maida mulki hannun farar hula ya kare ba tare da an cimma matsaya ba.
Hakan na nufin sojojin sun wuce wa'adin da kungiyar ECOWAS ta basu na su bayyana matsayar su kan batun.
Masu ruwa da tsakin sun tattauna batun tsawon lokacin da gwamnatin rikon kwarya kashe a kan mulki, da kuma takunkumin da a ka kakaba wa Malin.
Shugabanni daga kasashe takwas na yammacin Afirka, da wakilan majalisar dinkin duniya da na kungiyar tarayyar Afirka ne suka gudanar da taron a birnin Accra na kasar Ghana a jiya Talata. Da nufin kwakkwafe shawara, kan batun shirin mayar da kasar Mali kan turban mulkin dimokuradiyya.
Sun kuma bayyana fargaba cewa, matsalar tsaro da ake fama da ita a Malin ka iya kara dagulewa, ta kuma dama lissafin kokarin da ake yi na murkushe matsalar ta'addanci da ta yi katutu a rewacin kasar Malin.
Tun da farko kuma, shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS na yanzu, ya jaddada bukatar ganin kungiyar ta yammacin Afirka da shugabannin gwamnatin soja a kasar Mali, sun kai ga wata matsaya ta karshe wadda ba za a iya sauyawa ba, game da shirin mika mulki ga farar hula a kasar ta Mali.
Sai dai kuma a karshen zaman nasu na jiya, shugaban kungiyar ta ECOWAS, Nana Akufo-Addo ya shaida wa BBC, cewa ba su cim ma wata matsaya da shugabannin gwamnatin sojan ta kasar Mali ba.
ECOWAS a yanzu ta bukaci tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ziyarci Mali nan da mako guda, don ya ga irin ci gaban da aka samu, sannan ya dawo mata da bayani.
A ranar Asabara da ta gabata ce, gamayyar kungiyoyin farar hula da jam'iyyun siyasa ta kasar, ta yi watsi da matakin sojoji kan batun samar da gwamnatin rikon kwarya, wadda za ta kwashe tsawon watanni goma sha takwas kan mulki, da yiwuwar nada sojoji a matsayin shugabanninta.
Ana dai hangen kungiyar ta ECOWAS ka iya sanya wa Malin karin takunkumai, idan har aka kasa cimma wata yarjejeniya.











