Muhammadu Sanusi na II: Rashin zuwan El-Rufa'i taron NBA asara ce ga lauyoyi

Sarki Sanusi II da gwamna El Rufa'i

Asalin hoton, @GovKaduna

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Tsohon Sarkin Kano Sanusi na II ya ce bai ji dadin takaddamar da ake ba tsakanin kungiyar lauyoyin Najeriya da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai musamman kan matakin da NBA ta ɗauka na janye gayyatar da ta yi wa gwamnan ta halartar taronta.

Muhammadu Sanusi II ya bayyana haka ne lokacin ziyarar da ya kai wa gwamna inda ya ce ce ziyarar ta zumunci ce zuwa ga abokinsa wacce ba ta da wata nasaba da takaddamar da gwamnan yake yi da NBA.

Ziyarar tsohon Sarkin a Kaduna wacce ita ce ta farko da ya kai a wata jiha a Najeriya tun bayan cire shi daga gadon sarautar Kano, ta ja hankalin ƴan Najeriya musamman a shafukan intanet musamman a lokacin da ake ce-ce-ku-ce kan janye goron gayyatar da ƙungiyar lauyoyin Najeriya ta yi wa gwamnan.

Tsohon Sarkin wanda ya ce gwamna El-Rufa'i amininsa ne ya kuma ce ziyayar da ya kai masa ta zumunci ce da nuna godiya da tsayawa bisa ƙaunar da ya nuna masa kuma ba ta da nasaba da NBA.

Yadda zargin keta haƙƙin dan adam da kasa magance kashe-kashe a kudancin Kaduna da ƙungiyar lauyoyin ta yi wa El-Rufa'i ya ja hankalin ƴan Najeriya haka ma ziyarar da tsohon Sarkin Kano ya kai wa gwamnan na Kaduna.

A bidiyon da gwamna El-Rufa'i ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon Sarkin na Kano ya ce bai ji dadin takaddamar ba musamman matakin da NBA ta ɗauka na janye gayyatar da ta yi wa gwamna El Rufa'i.

Kauce wa Facebook

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook

"Na karanta zargin da suke, ina ta neman takaimaimai zargin da suke. Idan kun ce wani ba ya munta doka, to ta yaya yake ƙin mutunta dokar. Idan kuka ce wani ya kasa magance rikici, ta wace hanya?"

Sarkin ya ce yana fatan wannan takaddamar ba za ta rikiɗe ba ta koma ta addini ko ƙabilanci.

Tsohon Sarkin ya ce kamata ya yi ma Ƙungiyar lauyoyin ta bari sai ya halarci taronta ta yi masa wannan ƙorafin da inda take ganin ya gaza da waɗanda suka dace kuma don ya kare kansa.

Ya ce Ƙungiyar Lauyoyin ta yi hasara, domin halartar gwamnan zai ƙara ƙayatar da taronta kuma za su ƙaru sosai da fahimtar aikin da yake yi.

Waɗannan kalaman tsohon sarkin ne suka ja hankali a twitter, inda wani ɗan majalisar wakilai ya ce shawarar tsohon sarkin za ta kasance gaba da gaba da za ta iya kunyata gwamnatin Kaduna da kuma ƙungiyar lauyoyin.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Wasu kuma ƴan Najeriya na ganin kamata ya yi ƙungiyar ta lauyoyi su bari gwamnan ya halarci taron idan ma da wani ƙorafi sai ya kare kansa amma ba wai su ɗauki mataki ba.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Wasu kuma ganin El-Rufa'i ya gayyaci abokinsa ne tsohon sarkin Kano don ya kare shi.

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Presentational white space

Alaƙar Sanusi II da El-Rufa'i

Sarki Sanusi II da gwamna El Rufa'i

Asalin hoton, @GovKaduna

Sanusi II ya ce tun suna samari ƴan shekara 16 zuwa 17 yake tare da Nasir El-Rufa'i. " Shi mai kishin kasa ne wanda bai taɓa alaƙa da masu nuna ƙabilanci ba ko fifita addini.

"Dukkanin abokanmu ƴan Najeriya ne, wasu ma ba su tunanin mu ƴan arewa ne saboda mu ƴan Najeriya ne," in ji Sanusi II.

Kwanaki kaɗan ne bayan tube tsohon sarkin daga sarauta gwamna El-Rufai ya ba Sanusi II muƙaman shugaban jami'ar Kaduna da kuma mataimakin shugaban hukumar bunƙasa zuba jari ta jihar.

Kuma gwamna El-Rufa'i har ƙauyen Awe a jihar Nasarawa ya kai wa Sanusi II ziyara inda gwamnatin Kano ta tura shi bayan tube shi.

Presentational white space