Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
WAEC: Ɗalibai a Najeriya sun soma jarrabawar kammala sakandare
Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Makarantar Sakandare Ta Afrika Ta Yamma WAEC ta gargaɗi ɗalibai cewa satar amsar Jarrabawar Lissafi da ke yawo a shafukan sada zumunta ta jabu ce.
Hukumar WAEC ta shaida wa sashen Pidgin na BBC cewa masu zamba ne suka samar da irin waɗannan takardun jabun inda suke so su yi amfani da su don karɓar kuɗaɗe daga hannun mutane.
A yau Litinin ɗaliban ajin ƙarshe na sakandare a faɗin Najeriya ke soma rubuta jarrabawarsu ta kammala karatu bayan da aka samu jinkiri na watanni saboda annobar cutar korona.
Ɗalibai fiye da miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar ne ake sa ran za su ɗauki tsawon makwanni suna rubuta jarrabawar da ake kira WAEC wadda kuma a kan yi a wasu ƙasashen yammacin Afirka.
''Duk wani ɗalibi da ya karɓi takardun jabun zai sha mamaki a yayin da ya shiga ɗakin jarrabaw ya ga ta sha bamban da wacce za a ba shi,'' in ji WAEC.
Mai magana Hukumar da yawun WAEC Demianus Ojijeogu ya ce ɗliban Ghana ba su zana jarrabawar Lissafi ta WAEC ta bana ba kamar yadda mutane ke faɗa.
WAEC ta faɗi haka ne bayan da aka yi ta yaɗa jita-jitar cewa irin tambayoyin da aka yi w ɗaliban Ghana ne za a yi wa na Najeriya a takardar jarrabawar.
"Na ga takardu uku na jabu a jiya,'' in ji Mr. Ojijeogu.
Ɗaliban za su fara rubuta jarrabawar Lissafi ne a yau Litinin 17 ga watan Agustan, 2020 a faɗin ƙasar.
Kusan mako biyu kenan da ɗaliban da ke shirin rubuta wannan jarrabawa suka koma makaranta domin sake kimtsa kansu.
Cutar korona ce ta haifar da tsaikon soma rubuta jarabawa sakamakon rufe makarantu tun daga watan Maris zuwa Yuli.
Masu makarantu sun alƙawarta shirya jarrabawar bisa dokokin da aka tanadar don yaƙi da cutar korona, da suka haɗa da bai wa juna tazara a ɗakunan zana jarrabawar.
Nasara a jarrabawar WAEC ce ke tabbatar da kammala sakandaren ɗalibi da ba shi damar shiga jami'a da makarantun gaba da sakandare.
Najeriya ce dai ƙasar da ta fi yawan dalibai da ke rubuta wannan jarrabawar a makarantu sama da dubu 19 a da ke faɗin kasar.
Har yanzu dai jami'o'i da makarantun gaba da sakandare na ci gaba da kasancewa rufe a kasar.
Ministan ilimi a Najeriya, Chukwuemaka Nwajiuba ya ce mahukunta za su tabbatar komai ya tafi daidai ta fannin ɗalibai har zuwa jami'a ba tare da samun koma baya ba.
Ga yadda jadawalin jarrabawar WAEC ta 2020 yake