Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Korona da motsa jiki: Shin Covid 19 ta haifar da annobar ragonci?
- Marubuci, Daga Fernando Duarte
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 8
Shar Reid ba ta kasance a wuri mai walwala ba a lokacin da annobar COVID-19 ta bulla.
A kwanan nan ta koma wani birni a Birtaniya domin ta ci gaba da horonta na zama lauya sannan ta baro iyalai da ƙawayenta a gida yayin fafutukar.
Ta killace kanta a gida sakamakon cutar asma da ta ke fama da ita a lokacin zaman kulle.
"Na ji ƙasƙanci, ga ni a kebe kuma tsorace. Abun da na ke iya yi shi ne kallon tashar fina-finai a talabijin domin ba na iya fita," Kamar yadda Shar ta shaida wa BBC.
Ya ƙara da cewa "ƙididdigar yawan taku na abun tsoratarwa ne, wani lokacin nakan yi kamar taku 2,000 a rana guda."
Koda yake akwai muhawara game da ƙirga yawan taku a matsayin ma'aunin tantance ƙoshin lafiya sannan shawarar masana kiwon lafiya ta kwanan nan ita ce tsananin motsa jiki na da muhimmanci fiye da yawan yin shi, bincike ya nuna cewa yawan ƙididdigar taku na da nasaba da koshin lafiya.
A mafi ƙuncin lokaci na rayuwarta, Shar mai shekaru 30 kyakkyawar misali ce ta"annoba mai sanya ragontaka" ta sanya kwararrun masana kiwon lafiya fargaba kasancewar aukuwarta sakamakon zaman kulle ne a ɗaukacin faɗin duniya.
Raguwar yaɗuwar cutar a duniya- kuma ba samun sauƙi
Cikin wani cikakken bincike da aka gudanar ya zuwa yanzu, manhajar da ke tantance yawan motsa jikin da mutane suke yi Fitbit ta yi sharhi game da bayanan masu motsa jiki miliyan 4 a duniya baki ɗaya da suke yin amfani da manhajar cikin watanni biyu mabanbanta - Maris da Yuni.
Ta samu matsaikacin takun da mutane suka yi a lokacin zaman kullen ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da irin waɗannan lokutan na shekarar 2019.
Mafi muhimmanci shi ne, idan an kalli bayanan na watan Yuni, masana kimiyyar bayanan Fitbit sun kuma samu cewa har yanzu mutane ba sa motsa jiki dai-dai da yadda suka yi a irin wannan lokaci na shekarar da ta gabata ko da a yankunan da aka sassauta ko aka ɗage dokar zaman kullen.
Ga dukkan kashe-kashen rukunin mutane, matasa (masu shekaru18 zuwa 29) su ne suke da ƙarancin matakan motsa jiki.
"Matakai na sama game da yanayin takuruwa na iya shafar baccinmu wanda ka iya sanya mu jin kasala da gajiya, sannan daga bisani ya rage mana kuzari ta hanyar sanya mu motsa jiki kadan," a cewar Punam Krishan, likita kuma shugabar wata ƙungiya ta British Society of Lifestyle Medicine.
"Idan ba ma motsa jiki, mukan yi wautar zaɓen abinci maras inganci da ka iya sanya mu cikin haɗarin da zai shafi lafiyar jikinmu, da tunani, da kuma hankalinmu a rayuwa."
Tsoron ƙaruwar cututtuka
Dr Krishan sananne ne tsakanin masana kimiyya da shahararru a ɓangaren kiwon lafiya da suke da tsoron ganin yawan raguwar ƙoshin lafiya na iya biyo bayan ƙaruwar matsanantan cututtuka masu dangantaka da rashin motsa jiki, da suka ƙunshi ƙiba da yanayin zuciya.
Haka ma, an tabbatar da wasu cikin waɗannan yanayin ka iya sanya mutane ƙara shan wahalar illolin cutar korona - inda ake samun wasu rahotanni na yiyuwar sake ɓarkewar cutar a sassan duniya masu yawa.
Sai dai akwai manyan illoli.
Kasashe da dama sun ba da rahoton cewa matakan zaman kulle sun haifar da ƙaruwar masu kiba tsakanin al'ummarsu a wani lokaci - a kasar Brazil, ga misali, binciken da UFMG ta gudanar, guda cikin manyan jami'o'in kasar, ya nuna cewa kusan mutum hudu cikin 10 sun ƙara ƙiba yayin annobar.
Italiya da Fransa da Birtaniya da kuma Isra'ila wasu ƙasashen ne da suka bayar da rahoton ƙaruwar masu ƙiba a lokacin zaman kullen.
Rashin motsa jiki da annobar ta haifar abun damuwaa ne har ga Hukumar Lafiya ta Duniya, wadda ta fara fadakarwa mai taken #LafiyaAgida tare da sauƙaƙan hanyoyin motsa jiki da yawan motsa jikin da ake buƙata ga jerin rukunin al'umma.
Abin damuwa a Mexico
Bari mu ɗauki ƙasar Mexico, ga misali. Ita ce kasa da aka samun mafi yawan raguwar ƙidayar taku tsakanin kasashen da aka gudanar da bincike a cikinsu.
Bayanan Fitbit sun nuna - raguwar kusan kaso 80 cikin ɗari a watan Yunin shekarar 2020 idan aka kwatanta da irin wannan lokacin a shekarar bara.
Mexico a yanzu ita ce ƙasa ta uku mai mafi yawan mutanen da cutar korona ta kashe (sama da mutane 53,000 a ranar 11 ga watan Augusta). Sama da kaso 70 cikin ɗari na mamatan sun yi fama da cututtuka irinsu hawan jini da ciwon suga da kuma teba a baya.
Akwai damuwa ta musamman game da yawan masu ɗauke da cutar -da waɗanda suka mutu - a tsakanin yara.
Yawan waɗanda suka ƙara kamuwa da cutar ya ƙaru daga 84 zuwa sama da 2,600 tsakanin ranar 12 ga Aprilu zuwa 8 ga Yuni kaɗai, ƙididdigar da aka samu daga ma'aikatar Kiwon Lafiyar Mexico ta nuna- UNICEF, hukumar da ke kula da ƙananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, ta binciki matasan Mexico 8,000 ƴan shekaru 13 zuwa 30 sannan ta samu kusan rabinsu ba kasafai suke motsa jiki ba yayin annobar.
"Mafi yawansu ba su zuwa makaranta ko kuma suna tsoron fita daga gidajensu," a cewar Mauro Brero, jami'in UNICEF kan abinci mai gina jiki.
"Tuni Mexico ta shiga cikin jerin kasashen da suke da mafi yawan yara da matasa masu fama da teɓa kafin bullar annobar.
Abubuwan na iya ƙara muni a yanzu sannan su bar matasa cikin hadari," inji masanin.
Nazarin Fitibit ya nuna cewa ko da ƙasashen da ba su sanya cikakkiyar dokar kulle ba, duk da haka sun samu raguwar masu kirgen takunsu: a Japan, motsa jiki cikin watan Yuni ya tsaya a kaso 11 cikin dari ƙasa da yadda yake a shekarar 2019.
Alƙalumman sun nuna mutane ba su tsira sosai ba kamar kullum.
Hakan na da ci gaba na musamman ga dattawan Japan: masu bincike daga Tokyo-a Jami'ar Tsukuba sun gano "raguwa mai tarin yawa" a lokutan motsa jiki tsakanin tsofaffi a yayin annobar - sama da kaso 28 cikin ɗari na mutanen Japan na tsakanin shekaru 65 ne zuwa sama.
Sun kuma yi gargaɗin ƙaruwar samun nakasassu masu yawa nan gaba kadan.
Ciwon suga a Indiya na haifar da damuwa
A Indiya, matsaikacin kiɗayar taku shi ma kaso 11 ne cikin ɗari ƙasa da na watan Yuni, akwai fargaba game da "annobar ciwon suga" a ƙasa guda cikin ƙasashen da suka fi kamuwa da wannan cuta - an yi ƙiyasain cewa sama da Indiyawa miliyan 70 suna da ciwon suga, ƙasa ta biyu bayan China.
Tawagar likitoci mazauna New Delhi-da ke bibiyar masu ɗauke da ciwon suga sama da 100 yayin annobar sun samu ba kawai cewa da yawansu (kaso 42 cikin dari) sun rage motsa jiki ba ne kawai amma kuma suna cin ƙarin abinci mai gina jiki - abincin da ba a son mai cutar suga ya dinga ci.
"Annobar ta ɓulla a Indiya a lokacin da tuni mutanen ƙasar ke fama da rashin motsa jiki da kuma karuwar cututtuka,"Aman Dhall, mai tsara dabarun motsa jiki ta kafar yanar gizo a India, ta bayyana.
"A shekarar 2016, tuni wani binciken Hukumar Lafiya ta Duniya ya nuna cewa kaso 35 cikin ɗari na Indiyawa ba sa motsa jiki yadda ya kamata."
Ya ƙara da cewa"A sauƙaƙe mun fi yin fice ne a kallon wasanni kawai amma ba a yin su,"
Dhall ya yi amannar zaman kullen "ya sanya Indiyawa kin motsa jiki."
Mutanen da suke cikin haɗari ma "sun dakatar."
ƙaruwar haɗarin kamuwa da cututtuka ko kuma ƙara zama mai saukin kamuwa da cutar Covid-19 da alama ba sa zaburar da mutane tashi tsaye don tunkarar kalubalen.
Wannan shi ne matsayin da Nina Rogers ta cimmawa, wadda masaniyar yaɗuwar cututtuka da magance su ce a Jami'ar birnin Landan wadda ta ke yin aiki tare da takwarorinta na jami'ar Bath don yi wa manyan mutane ƴan Birtaniya sama da 5,800 ƴan shekaru 20 zuwa sama tambayoyi a lokacin annobar.
Mafi yawan mutane (kaso 60 cikin ɗari) sun ce sun ci gaba da yadda suke motsa jikinsu, sannan kusan kaso 25 cikin ɗari ne kacal suka tabbatar sun rage yawan yadda suke yi a baya.
Matsalar ita ce, ƙarin mutane da ke fama da wasu cututtukan da suka sanya su cikin haɗarin kamuwa da cutar Covid-19 suna cikin mutanen da suka dakatar."
"Hakan bai zo da mamaki ba," inji Rogers.
"Abun damuwar shi ne. zamu iya samun wasu karin zaman kullen da za su iya tsawaita lokacin ƙarancin motsa jiki.
"Hakan zai kara yawan mutanen da za su kasance cikin matsanancin haɗarin kamuwa da cutur korana."
Komawa ga motsa jiki ? ba sauki…
Amma kuma kaucewa "illar zaman kullen" ya fi sauki a faɗa a baki fiye da aiwatarwa.
Abueng Sekgwelea, mazauniyar Johannesburg ce- da ke koyar da wasan taekwondo da motsa jiki, ta faɗa wa BBC cewa abu ne mai sauki ga mutane su rasa ƙwarin gwiwa a lokuta irin waɗannan.
"Ba dai-dai mutane suke yi ba a hankalce- wasu da na ke horaswa na damuwa game da samun abincin da ya dace kafin su fara tunanin motsa jikin," a cewar Sekgwelea.
"Ba dai-dai mutane suke yi ba a hankalce- wasu da na ke horaswa na damuwa game da samun abincin da ya dace kafin su fara tunanin motsa jikin," a cewar Sekgwelea.
"Amma yana da matuƙar muhimmanci mu kula da juna. Wata ƙawata da ba ta motsa jiki akai-akai ta samu larurar shanyewar rabin jiki a lokacin kullen."
Tuni mai horas da dabarun motsa jikin ta taimakawa ƙawarta yayin kokarin samun sauki.
Sekgwelea ta ce "Nauyinta ya ragu da kilo 10 tun da na fara aiki tare da ita,"
Wani dubarun karkatar da hankali ne daga ɓangaren mai horas da dabarun motsa jikin na kanta: ba ta dalibai sannan ba kuɗin shiga a lokacin saboda taƙaitawar ta wannan lokacin a Afrika ta kudu.
"Ta shafi tunani na fiye da na kudi. Dole na tabbatar na ci gaba da motsawa."
"Don haka, na yi amfani da matakalar bene domin motsa jiki na, ga misali - ina son nunawa mutane cewa ba sa buƙatar dakin motsa jiki kafin su iya motsa jikinsu."
Labarin Shar
Kun tuna Shar Reid, mai fatan zama lauya?
Ta kuma jajirce.
Ta fara da shirin zaman kulle na Youtube da kan motsa jiki da ƴar Birtaniya Joe Wicks ta samar, ta dakatar da abun da ta ke yi sannan ta ke yin tafiya mai nisa zuwa ƙauyukan da suke kusa da gidanta.
(hotunan Shar na shafinta na Instagram na nuni da yadda ta ke motsa jikinta a lokacin zaman kulle)
Labari ne da Shar ta bayar a shafinta na Instagram, tare da hotunanta da ba ta ɗauka da manufar aka saba ba amma kuma sun kunshi bayanan karfafa gwiwa da ta yi fatan zaburar da sauran mutane da su.
"Mafi yawancin ƙawayena suna shaye-shaye da ciye-ciye a lokacin zaman kullen," a cewarta.
"Kasancewata cikin rukuni mai haɗari saboda cutar asma, na bukaci in kare kaina."