Yadda ƙasashe ke kallon ƙawancen diflomasiyya tsakanin UAE da Isra'ila

Asalin hoton, AFP
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta zama ƙasar Larabawa da ke yankin Gulf ta farko da ta ƙulla yarjejeniyar daidaita alaƙa da Isra'ila - ƙawance irin na zaman lafiya.
Yarjejeniyar da aka yi wa laƙabi da "Abraham Agreement", wadda Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar ranar Alhamis na nufin Isra'ila za ta dakatar da yunƙurin da take yi na mamaye wani yanki na Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Sai dai a jawabin da ya yi wa 'yan jarida daga bisani a Tel Aviv, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ya amince ya jinkirta matakinta na mamaye yankin a wani ɓangare na yarjejeniyar da aka cimma da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa amma ana ci gaba da shirye-shirye.
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ce kuma ƙasar Larabawa ta uku da ta cimma irin wannan yarjejeniyar da Isra'ila bayan Jordan da Masar.
Ga dai yadda sauran ƙasashe da masu ruwa da tsaki a rikicin tsakanin Isra'ila da Falasɗinu suka kalli wannan yarjejeniyar:

Shugabancin Falasɗinu
Cikin wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Shugaban Falasɗinu Mahmoud Abbas ya yi tur da yarjejeniyar.
"Shugabancin Falasɗinawa ya yi watsi da yarjejeniyar tare da yin tur da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Isra'ila da Amurka," a cewar Nabil Abu Rudeineh, wani babban mashawarcin Abbas.
Da yake karanto wani ɓangare na sanarwar a wajen fadar shugaban ƙasa da ke Ramallah a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, Abu Rudeineh ya ce yarjejeniyar "cin amanar Ƙudus da Al-Aqsa da kuma Falasɗinawa ne."
Hamas
Ƙungiyar Hamas ta ƙi amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wadda aka ƙulla don Isra'ila ta ajiye ƙudirinta na mamaye Gaɓar Yamma da Kogin Jordan - abin da ta ce bai zo dai-dai da buƙatun Palastinawa ba.
"Wannan yarjejeniya ba ta biya buƙatun Falasɗinawa ba. Yarjejeniyar tana goyon bayan Isra'ila ta ci gaba da take hakkokin al'ummar Falasɗinu sannan ta ci gaba da aikata miyagun alifuka kan jama'armu," in ji mai magana da yawun Ƙungiyar Hamas Hazem Qassem cikin wata sanarwa.
"Abin da ake buƙata shi ne a goyi bayan fafutukar da mutanenmu suke yi na dakatar da mamayar sannan kada a ƙulla wata yarjejeniya da mai mamayar."

Jordan
Jordan ta ce yarjejeniyar na iya sa a ci gaba da tattaunawar sulhu idan har ta yi nasarar jan hankalin Isra'ila ta amince da samar da ƙasar Palastinu a yankin da ta mamaye lokacin yaƙin ƙasashen Larabawa da Isra'ila a shekarar 1967.
"Idan Isra'ila ta kalli lamarin a matsayin wani abu na kawo ƙarshen mamaya....hakan zai kai ga samun zaman lafiya a yankin," a cewar ministan harkokin waje Ayman Safadi cikin wata sanarwa.
Gazawar Isra'ila ta yi hakan ba abin da zai haifar sai ƙara rura rikicin da aka shafe gwamman shekaru ana yi tsare da barazanar tsaro a yankin baki ɗya, kamar yadda Safadi ya faɗa.
Masar
Shi kuwa Shugaban Masar, Abdel Fattah el-Sisi, abokin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa maraba ya yi da yarjejeniyar.
"Na bibiyi sanarwar da Amurka da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Isra'ila suka fitar kan dakatar da mamaye filayen Falasɗinawa da ɗaukan matakan kawo zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya," a cewar el-Sisi a shafin Twiiter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
"Ina girmama ƙoƙarin da waɗanda suka yi ruwa suka yi tsaki a cimma yarjejeniyar don kawo daidaito a yankinmu." in ji el-Sisi.

Burtaniya
Firaministan Burtaniya Boris Johnson ya bayyana jin daɗinsa kan cimma yarjejeniya tsakanin Isra'ila da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
"Matakin UAE da Isra'ila na gyara alaƙarsu labari ne mai daɗin gaske," kamar yadda Johnson ya faɗa a Twitter.
"Yarjejeniyar dakatar da ƙudirin mamaye yankin babban ci gaba ne da zai kai ga samun zaman lafiya a gabas ta tsakiya."
Faransa
Faransa ma ta yi maraba da matakin Isra'ila na janye shirin mamaye yankunan Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ƙarƙashin yarjejeniyar da aka cimma mai dumbin tarihi, yana mai bayyana ta a matsayin ci gaba, a cewar ministan harkokin waje Jean-Yves Le Drian.
Ƙawancen ya ba da damar komawa teburin tattaunawa tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa da nufin kafa ƙasashe biyu, abin da ya ce shi ne zaɓi ɗaya tilo na samar da zaman lafiya a yankin.
Iran
Kamfanin dillancin labarai a Iran, Tasnim da ke da alaƙa da dakarun juyin-juya halin Musulunci wato IRGC ya ce yarjejeniyar tsakanin Isra'ila da UAE abin "kunya" ne.
Jagororin Iran ba su ce komai ba game da yarjejeniyar.
Yarjejeniyar tsakanin Isra'ila da UAE ba za ta samar da zaman lafiya ba a yankin, cikin saƙon Twitter da mashawarci na musamman kan harkokin ƙasashen duniya ga shugaban majalisar dokokin Iran.

Asalin hoton, AFP
Joe Biden
Cikin wata sanarwa, ɗan takarar shugaban Amurka ƙarkashin jam'iyyar Dimokrat Joe Biden ya ce: "Tayin UAE na amincewa da ƙasar Isra'ila babban ci gaba ne.... Gwamnatin Biden da Harris za ta ɗora kan wannan ci gaba kuma za ta ƙalubalanci duka ƙasashen yankin su marawa batun baya."
Biden ya kuma ya magana kan mamaye yankin: "Mamaya babbar barazana ce ga zaman lafiya, dalilin ke nan da ya sa nake sukar shi kuma zan soke shi ko da na zama shugaban kasa," a cewarsa.
Majalisar Ɗinkin Duniya
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi maraba ga "duk wani ƙoƙari da zai haifar da zaman lafiya da tsaro a yankin gabas ta tsakiya," kamar yadda wani mai magana da yawun Majlisar Ɗinkin Duniya ya shaida.












