An kama limami kan zargin daƙile ƙoƙarin shawo kan cutar korona

Asalin hoton, EPA
An kama jagoran addinin da aka ambato sunansa cikin batun ɓarkewar cutar korona na farko-farko a ƙasar Koriya ta Kudu bisa zargin kawo cikas a ƙoƙarin shawo kan cutar.
Ana zargin Mista Lee Man-hee, mutumin da ya assasa cocin Yesu ta Shincheonji da gabatar da bayanan ƙarya game da wurin taruka a watan Fabrairu da kuma yawan mahalarta.
A lokacin, idon duniya na kan Koriya ta Kudu, inda ɓullar cutar korona kan mutane da dama da aka fara samu a wani wuri da ba China ba, ke ci gaba da ƙaruwa cikin hanzari.
A jimilla, kimanin mabiyan cocin dubu huɗu ne suka kamu da cutar. A wani lokaci, sai da suka kasance rabi na adadin masu fama da korona a ɗaukacin Koriya ta Kudu.
A watan Maris, Mista Lee ya nemi afuwa kan rawar da ɓangarensa ya taka wajen yaɗuwar ƙwayar cutar, har ma sai da ya durƙusa a kan gwiwoyinsa ya sunkuyar da kai yayin wani taron manema labarai.
Da yake jawabi game da shawarar tsare shi, wani alƙali ya ce akwai hujjojin da ke cewa ana lalata wasu shaidu masu alaƙa da binciken da ake yi kuma lamarin na iya ci gaba.
Akasari Koriya ta Kudu ta yi nasarar shawo kan ƙwayar cutar korona ta hanyar bin sawu da ganowa. Sai dai kuma ana ƙara samun bazuwar cutar wadda masu cutar da ke shiga ƙasar ke daɗa haɓaka ta.






