Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
NITDA ta bai wa nakasassu horo kan fasahar sadarwa a Kano
Hukumar bunkasa fasahar sadarwar zamani ta Najeriya NITDA, ta horar da nakasassu 30 a Jihar Kano ilimin fasahar sadarwa a wani yunkuri na bunkasa bangaren.
An horar da nakasassun ne wadanda ke da nakasa daban-daban sana'oi iri daban-daban.
An shafe kwana biyar ana ba su wannan horon, wanda aka kammala a ranar Asabar, 25 ga watan Yulin 2020 a birnin na Kano.
Da yake jawabi a yayin kammala horarwar, Ministan Sadarwa na Najeriya, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami, ya shawarci wadanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da abin da aka koya musu domin ci gabansu dama al'umma baki daya.
"Ba a nakasassshe sai kasasshe, don haka kada ku bari nakasarku ta sanyaya muku gwiwa, dole ku tashi ku nemi na kanku ta yadda za ku zamo masu dogaro da kanku," in ji ministan.
Daya daga cikin wadanda suka samu wannan horo, a madadin sauran, ya nuna matukar godiya da wannan horo da aka ba su, inda ya yi alkawarin za su yi amfani da abin da suka koya wajen gina kansu da ma sauran al'umma.
An bai wa wadanda suka amfana kyautuka bayan kammala horon.