Coronavirus a Najeriya: Annobar ta tilasta min yin aure ta intanet a Najeriya

    • Marubuci, Daga Celestina Olulode
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

''Zan so nan da shekara 20 na ci gaba da tunawa da wannan rana ta bikinmu....Ba saboda annobar korona ba, sai dai saboda na zabi na karkare rayuwata da Reme.''

Ayokunle Sulaiman da buduwarsa Reme Olotun na ta lissafin lokacin bikinsu da aka tsara gudanawar wa a otel din Sheraton da ke Legas din Najeriya, a ranar 18 ga watan Afrilu.

Ta'azzarar da annobar ta yi ya jefe Reme da ke aiki a Canada cikin damuwa, saboda ba za ta iya zuwa Najeriya ta auri masoyinta Marry Ayokunle ba.

''Na shiga kaduwa sosai,'' kamar yadda ta shaida wa BBC. ''Na riga na sayi kayan fitar biki, takalmi, da duk abin da nake bukata na bikin.''

Sai dai a nasa bangaren, batun dage bikin ba abu ne da Ayokunle zai aminta da shi ba. Don haka sai ya shiga wasa kwakwalwa domin samar da mafitar yadda za a yi bikin.

A karshe dai masoyan junan sun yanke shawarar a yi daurin aure, ranar 18 ga watan Afrilu wanda fasto ya jagoranta ta manhajar zoom a Intanet.

''Yanayi ne na rashin jin dadi da karfafa gwiwa, kyakkyawan zato da fushi da kuma yarda da cewa komai zai tafi daidai,'' a cewar Reme.

''A ko da yaushe kana da mafitar kowanne irin yanayi da ke sanyaya mun zuciya,'' kalaman da ta fada wa mijinta kenan a lokacin.

Biki ta intanet ya halasta?

A Najeriya babu tanadin dokar aure ta intanet.

Dokar aure a kasar, ta bai wa masoya zabi biyu - aure ta hanyar rijista a kotu, ko kuma ta hanyar addini a amintaccen wurin ibada.

Sai dai saboda dokar kulle da hana gudanar da taruka, wata lauya Abisola Ogunbadejo ta ce mutanen da ke shirya bukukuwa na ta aiko tambaya kan ko biki a intanet ya halasta.

Ta yanke hukuncin yin wani bidiyo a YouTube da ke ba da shawarwari.

Ms Ogunbadejo ta ce duk da cewa gudanar da biki bisa addinin ta intanet na iya gamsar da wasu, yana da muhimmanci mutum ya kara da auren kotu cikin gaggawa saboda hali na mutuwa ko akasi da ka iya tasowa nan gaba.

Da fari, Ayokunle da Reme sun shirya domin gudanar da bikinsu, idan Reme ya samu damar zuwa Najeriya, kafin su koma Canada baki daya, amma korona ta haifar da akasi.

Sai dai a karon farko kasancewarsu ma'aurata kamar yadda suka yanke shawara ya sanya su farin ciki. Ko da mutane za su yi musu kallon aurensu bai halarta bisa doka ba, auren da suka yi ta intanet ya basu damar bayyana soyayarsu ta hanya daban.

''Zan ci gaba da murna zagoyarwar wannan rana saboda ita ce ta bikina,'' a cewar Ayokunle. ''Ni yanzu Reme ta zama matata kuma ina kiranta matata wanda hakan shi ne abu mafi muhimmanci.''

Reme ta ce da farko ita kanta ta shiga tababa kan bikin intanet, amma hakan ya kasance burin Ayokunle kuma ya fahimtar dani don amincewa da hakan.

''Ya hadu yana da hikima, saboda ya tsara komai don ganin burinmu ya cika.''

Ma'auratan sun yi rantsuwa, sun saurari wa'azin fasto kan muhimmancin aure, mu saurari shawarwari da fatan alheri daga abokanmu, sannan mun yi rawa a matsayin ma'aurata a karon farko.

Bisa muradanmu

Ga 'yan Najeriya da dama biki babban taro ne, ana kashe kudi sosai sannan wasu iyalai na kashe dubban daloli kan shagulgula da kyaututtuka. A ra'ayin Reme, gudanar da wannan biki ta intanet ya yi daidai.

''Lokaci ya yi da za mu soma tsara abubuwa yadda muke so don kanmu - ba a raba mutane da abin fada.'' a cewarta.

Biki ta intanet na nufin masoya na iya toshe kunuwansu su mayar da hankali kan abin da ya fi muhimmanci.

''Ba burgewa ba ne ko tsari a ce za a dage biki saboda annobar korona,'' a cewar Adekunle.

''Ba wai batu ne kawai na taro ba - batu ne da ya shafi abin da muke son mu cimma shawarar da muka yanke a rayuwarmu na soma rayuwa a matsayin ma'aurata.''

Wasu labaran da za ku so karantawa:

Matsayinsu a yanzu ya sauya rayuwarsu da kuma yadda suke mu'amala.'' Bayan ranar 18 ga watan Afrilu ya zame mun tilas na bayyana Reme a matsayin matata.'' a cewar Ayokunle.

'Ba wai batun taron biki ba ne'

Ba su kadai ba ne mutanen da suka yanke shawarar gudanar da bikinsu ta intanet ba.

Mazaunan Legas Ademola da Yinka Adeleke sun gudanar da bikinsu bisa tsarin addini a ranar 18 ga watan Afrilu, amma wannan ya biyo bayan auren kotu da suka yi ranar 12 ga watan Disamban 2019.

Kasancewa suna da abokai da 'yan uwa a ketare, masoyan sun yanke shawarar shirya gagarumin biki a ranar 18 ga watan Afrilu. Sai dai saboda annobar korona sun yanke shawara bikin ya kasance ta intanet.

Ademola ta ce ita da Yinka da sun gudanar da bikinsu ta intanet da a ce basu yi auren kotu ba.

''Ina ganin yana da muhimmanci ku yi aure a coci. Fasto ya tabbatar da aurenku, amma lokacin zai fi dadi idan ya kasance baku yi aure ba.''

Sai dai sabbin ma'auranta sun ce masoya na da daman zabin abin da yafi musu sauki musamman a lokutan da ake cikin kalubale irin na annoba.

Fastonsu Bolaji Idowu, na ganin ya kamata a sauya dokoki saboda ''komai na iya tasowa wanda ba a shirya ba kuma dole a samar da mafita''.

''Ina ganin dokokin ya kamata su soma tunanin yadda za a tunkari irin wadannan matsaloli da yanzu ake fuskanta a rayuwa''.

Kasa da mutum 50 ne suka halarci bikin Yinka da Ademola da aka gudanar a intanet. Yinka ya ce bikin ya ja hankali sosai.

''Bayan bikin, mutane da dama sun tuntube ni, suna masu cewa: 'Kun burge mu kun kafa tarihi, duk kun sauya mana tunaninmu.'

''Akwai mutanen da suka yanke shawarar gudanar da bikinsu ta Zoom bayan sun ga hotunan namu bikin ta intanet.''

Ma'auranta sun ce za su gudanar da babban taro da abokansu da 'yan uwansu bayan sassauta dokar kulle, sai dai Yinka ya ce yana alfahari da cewa ba su matsawa kansu ba wajen bin al'adu da tsarin al'umma.

''Ba wai batu ne na taro ko yadda biki ya kasance ba. Wannn abu ne da ya shafe mu da aurenmu.''