Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaya ake baiko a Musulunci? Ga abin da addinin ya tanada
Jama'a da dama a kafafen sada zumunta na ci gaba da ce-ce-ku-ce kan bidiyon nan da ya karaɗe shafukan sada zumuntar, wanda wani saurayi a Kano ya durƙusa ya saka wa wata budurwa zobe a matsayin baiko.
Akasarin ra'ayoyin jama'a sun fi karkata ne kan fuskar addinin Musulunci, inda suke cewa ba haka ya kamata Musulmai su yi baiko ba ko kuma neman aure.
Mutane na zargin cewa masoyan biyu na kwaikwayar al'adu ne irin na Turawa a maimakon su tsaya kan al'adarsu ta Hausa da kuma koyarwar Musulunci.
Wacce hanya Musulunci ya tanada domin yin baiko?
Malam Umar Shehu Zaria, malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, kuma ya shaida wa BBC cewa akwai hanyoyin da Shari'ar addinin Musulunci ta tanada yayin neman aure.
Ya bayyana cewa irin bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta da sunan baiko "saɓon Allah ne kuma abu mai haɗari".
A cewarsa: "Baiko ba wani abu ba ne da ya zama tilas ko wajibi a aure, idan ba a yi shi ba babu wani abu da zai cutar a cikin al'amarin aure."
Aure a Musulunce wani babban al'amari ne kuma akwai hanyoyi da Shari'a ta tanada yayin nemansa da kuma bikin.
"Abu na farko da ya kamata namiji ya fara yi wurin neman aure shi ne neman yardar iyayen yarinya kafin ya fara nemanta, haka zalika tare da tabbatar da cewa yarinyar ita ma ta amince da mai neman nata," in ji Malam Umar.
"Idan mutum ya je nema za a iya ba shi damar ya yi magana da ita, idan sun fahimci juna Alhamudlillahi, idan kuma ba su fahimci juna ba to batun auren dole ba ya cikin addinin Musulunci."
"Ya kamata mutane su rinƙa taka-tsantsan da kafafen sada zumunta, domin yanzu za a iya wallafa cewa an yi aure kuma ba da daɗewa ba sai a saka an haihu, daga nan kuma sai a saka mutum ya mutu. Wannan na nufin rayuwa ba ta da tabbas."
Malam ya ƙara da cewa "bayyana tsiraici da cuɗanya tsakanin maza da mata da rungume-rungume lamari ne wanda babu shi tun asali a al'adar Bahaushe kuma rashin yin hakan ya taimaka wurin albarkar auren mutanen shekarun baya".
Ya bayyana cewa "sauyawa da kuma ɗauko al'adu waɗanda suka saɓa wa addinin Musulunci kan jawo mace-macen aure da dama da muke ganin yawaitarsu a yanzu".
Ko ci gaban fasahar sadarwa ya taimaka wurin sauya al'adun Bahaushe? Sharhi daga Mustapha Kaita
A halin yanzu, ana ganin cewa ci gaban da aka samu ta hanyar fasahar sadarwa ne ya sa al'adu da dama da mutane suka gada kaka da kakanni ke sauyawa.
Tun bayan da aka fara kallon tashoshin tauraron ɗan Adam ko kuma satellite, a hankali al'adun Hausawa suka fara sauyawa.
Misali, wasu jama'a saboda tsananin kallon tashoshin Indiya ya sa suke ɗabi'u da halaye irin nasu, ya zama ko waƙoƙin Hausa ba sa saurara sai dai na Indiya.
Su ma masu kallon tashoshi da fina-finai na Turawa abin ya shafe su, ya zamo cewa ɗabi'u da halayensu sun koma irin na Turawan. Salon maganarsu da suturar da suke sakawa har ma da abincin da suke ci sai duka irin na Turawa.
Bincike da wasu masana falsafa na Jamus, Theodor Adorno da kuma Max horkheimer suka gudanar kan kafofin talabijin da fina-finai, ya gano cewa tuni kafofin suka zama wurin "saye da sayar da al'adu."
Suna nufin mutum da kuɗinsa zai sayi al'adar wata ƙabila ta hanyar sayen fina-finansu ko kuma waƙoƙinsu.
A halin yanzu, za a iya cewa hakan ya zamo gaskiya ganin yadda duniya take a tafin hannunmu ta yadda da wayar salula mutum zai iya kallon al'adun mutane daban-daban na duniya kuma ya yi koyi da su matuƙar yana da data a wayarsa.
Kafafen sada zumunta irinsu Facebook da Twitter ne manyan dillalai a halin yanzu na saye da sayar da ɗabi'u.
A kafafen ne mutane daban-daban a faɗin duniya ke haɗuwa su yi musayar hotuna da bidiyo da batutuwa, idan al'adar wata kaɓila ta birge ta wata ƙabila daga nan sai a samu sauyin al'ada.
Yanayin ci gaban da aka samu a halin yanzu ya sa ba sai mutum ya je Amurka ko Indiya ko kuma Ingila ba zai fara koyon al'adarsu, mutum na zaune a gida sai ya koma Baturen ƙarfi da yaji.