Coronavirus a Ghana: Yadda gwamati ta kashe $9.3bn a dafa abincin tallafi yayin kullen korona

Asalin hoton, Fred Duhoe/Facebook
- Marubuci, Favour Nunoo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin, Ghana
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 1
Adadin kuɗin da gwamnatin Ghana ta kashe wurin samar da abinci a lokacin dokar korona na saka 'yan ƙasar suna tambayoyi domin irin maƙudan kuɗin da aka ce an kashe.
Ministan kuɗi na ƙasar Ken Ofori-Atta ya bayyana cewa gwamnatin ƙasar ta kashe kuɗi sama da dala miliyan tara wato cedi miliyan 54.3 wurin dafa abinci domin bai wa masu ƙaramin ƙarfi kusan 470,000 a cikin garin Accra da Kumasi yayin kullen da aka yi na makonni uku.
Daga cikin irin na'uin abincin da gwamnatin ta raba akwai shinkafa da kaza da kifi da dafa-dukar shinkafa da kuma wasu abubuwan da ba a rasa ba da aka ba masu ƙaramin ƙarfin.
Babu karin bayanai
Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.Karshen labarin da aka sa a Facebook


Ga ƙiyasin kudin da ake gani an kashe
Gwamnatin ta kashe cedi miliyan 54.3 kan iyalai 470,000 na kwanaki 21 domin abinci.
A kalla ba a ƙasaru ba kuɗin kwanon abinci da mutum zai ci ya ƙoshi a Ghana zai kai cedi 5.
Wanan na nufin an kashe cedi 5 sau kwanaki 21 cedi 105 ga duk mutum ɗaya.
Idan aka ce kuma cedi 105 sau 470,000 hakan zai bayar da cedi 49,350,000.
Abin da aka samu kan hakan shi ne cedi 49,350,000, idan aka cire wannan kuɗin daga cedi 54,300,000 zai bayar da cedi 4,950,000.
Idan aka yi lissafi, za a samu bambancin cedi 4,950,000.
Ba mu da tabbacin ko me aka yi da sauran wannan kuɗi, wata kila an yi amfani da su ne wurin jigilar abincin ko kuma wasu abubuwa na daban.
A ranar 27 ga watan Maris ne Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya saka dokar kulle a Accra da Kumasi domin daƙile yaɗuwar cutar korona.










