Coronavirus a Ghana: Abin da ya sa ba a rufe makarantu ba duk da yaɗuwar cutar

Asalin hoton, Getty Images
Iyayen yara a Ghana na ci gaba da kiraye-kiraye ga gwamnati cewa ta rufe makarantu ganin yadda cutar korona ke ci gaba da yaɗuwa.
Kungiyoyin Iyayen Yara da Malamai na kasar (NCPTAs) sun ce yara na cikin tsoro da fargaba saboda yadda suke jin labarin abokansu da suka kamu da cutar korona.
Alexander Yaw Danso, Shugaban kungiyoyin na NCPTA ya shaida wa BBC Pidgin cewa "Ghana ta fara ne da samun mutum ɗaya mai cutar zuwa biyu, a yanzu kuwa masu ɗauke da ita sun kai 24,000. So suke mu jira har sai watan Satumba?''
Ya ci gaba da cewa: "Babban abin haushin ma shi ne ba a yi wa ɗaliban gwajin cutar...ta yaya za su san ko sun kamu da ita idan ba sa yi musu gwaji?"
An fara nuna fargaba ne bayan an samu rahoton cewa wasu mutum 55 ciki har da ɗalibai da malamansu a makarantar sakandare ta Accra Girls' Senior High School sun kamu da cutar ta korona.
Hukumar Lafiya ta Ghana (GHS) da Hukumar Ilimi (GES) sun fitar da wata sanarwar haɗin gwiwa, inda suka bayyana cewa cikin mutum 314 da aka yi wa gwajin cutar, 55 sun kamu da ita.
GES ta ce za su ci gaba da yin gwajin tare da jinya da kuma bin sahun masu ɗauke da cutar a makarantun da ke faɗin ƙasar.
Mai magana da yawun hukumar GES, Cassandra Twum Ampof, ya bayyana wa BBC Pidgin cewa "mun gano tare da killace waɗanda suka yi mu'amala da masu ɗauke da cutar daga sauran ɗalibai.
Hukumar ta GES ta ce rufe makarantu ba abu ne mai kyau ba a wannan lokaci.
"Daga irin yadda muke kula da yanayin, mayar da ɗaliban gida ba shawara ce mai kyau ba," in ji Cassandra Ampofo.


Dalilan da GES ta bayar na ƙin rufe makarantun
- Ɗaliban sun kasance a ɗakunan kwanan ɗlibai ne saboda suna ƙoƙarin rubuta jarrabawarsu ta ƙarshe
- Zai fi kyau a ƙyale su a makarantu sama da mayar da su gida saboda za a fi kula da su a nan
- Gwamnati za ta fi samun sauƙin bin sahun waɗanda suka yi hulɗa da masu cutar tare da kula da masu ita
- Kasancewar ɗaliban sun fito ne daga sassan ƙasar, idan aka bari suka koma gida za su harbi al'ummomin yankunansu da cutar
Duk da irin kiraye-kirayen da Kungiyoyin Iyayen Yara da Malamai na kasar (NCPTAs) suka yi, Hukumar Ilimi (GES) ta ce ita ce ke da alhakin kula da ɗaliban da ke shirin rubuta jarrabawarsu ta ƙarshe.










