Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Dubun dubatar yara a Afrika na iya mutuwa saboda rashin allurar riga-kafi'
Wani sabon bincike ya ce dubun dubatar ƙananan yara ne a Afirka za su iya mutuwa matuƙar aka jingine shirye-shiryen alluran riga-kafin da ake yi saboda fargabar annobar korona.
Masu binciken da ke zaune a Burtaniya da Switzerland sun ce bai kamata hatsarin da ke tattare da kamuwa da cutar korona ya hana gudanar da gangamin alluran riga-kafi na lokaci-lokaci ba.
Masu binciken sun yi amfani da wani tsarin lissafin kwamfyuta don kwatanta yadda cutar korona ke yaɗuwa cikin dukkan ƙasashen Afirka 54.
Bisa ga yadda al'amarin yake a faɗin duniya, lissafin ya ƙaddara cewa kashi sittin cikin ɗari na kowacce al'umma, zai kamu da cutar COVID-19, lamarin da zai katse ayyukan kula da lafiya na a ƙalla tsawon wata shida.
Binciken ya gano cewa ci gaba da gangamin riga-kafi a kai a kai na cutuka irinsu ƙyanda da shawara da ciwon hanta na iya janyo mutuwar ƙarin yara dubu takwas ta hanyar annobar korona.
Sai dai, masu binciken sun ce akwai matuƙar hatsari ga rayuwar ƙananan yaran saboda katse alluran riga-kafin, lamarin da ka iya haddasa mutuwar yaro dubu ɗari bakwai.