Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Wane hali yaran da ba a yi wa riga-kafi ba a Najeriya ke ciki?
Annobar korona da ta bayyana a cikin watan Fabrairun wannan shekara kuma ta yi wa harkokin rayuwa illa, ciki har da bangaren kiwon lafiya.
Cikin watanni hudun da aka shafe ana fama da cutar, hukumomi a Najeriya sun dauki matakai da suka haɗa da kulle da hana zirga-zirga tsakanin yankunan ƙasar.
A cikin wannan halin ne kuma aka haifi dubban jarirai, waɗanda yawancinsu ba su sami kulawar da ta dace ba.
Ba a yi wa yawancin jariran allurar riga-kafi ba, matakin da ya sanya rayuwarsu cikin hadarin kamuwa da cututtuka masu yi wa ƙananan yara illa kamar zazzaɓin cizon sauro da ƙyanda.
Dakta Usman Shehu Adamu shi ne jami'i mai kula da alaƙar cutar korona da lafiyar yara ƙanana a hukumar lafiya a matakin farko ta kasar, kuma ya bayyana wa BBC halin da ake ciki kan wannan batu.
"Hukumar lafiya a matakin farko ba ta yi ƙasa a gwiwa ba tun da cutar korona ta bayyana a Najeriya ranar 27 ga watan Fabrairun wannan shekarar."
Ya ce sun san mutanen da ke halartar asibitoci za su ragu matuƙa saboda matakan kulle da gwamnati za ta ɗauka a ƙoƙarin daƙile yaɗuwar cutar.
"Babban shugaban wannan hukuma, wato Dakta Faisal Shu'aib ya kafa wani kwamiti na kar-ta-kwana da kuma wata cibiya ta samar da taimakon gaggawa a bangaren cutar korona," in ji Dakta Adamu.
Halin da ƙananan yara ke ciki
Wane hali jarirai da aka haifa cikin wata hudun da suka gabata har ma da ƙananan yara ke ciki saboda rashin karɓar allurar riga-kafi?
Ganin yadda cututtuka kan yi wa irin wannan rukuni na ƙananan yara illa, ƙasar na iya fuskantar koma baya idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba.
Dakta Adamu: "Duk yaron da bai karɓi allurar riga-kafi ba na cikin hatsarin kamuwa da cututtukan masu saurin kashe ƙananan yara kamar zazzabin cizon sauro da ƙyanda da kuma cutar pneumonia. Mata masu juna biyu ma ba su tsira ba"
Shawarar da malaman lafiya suke bayarwa shi ne duk waɗanda suka san ba a yi wa ƴaƴansu allurar riga-kafi cikin wannan lokacin ba, sai su kai yaran asibitocin da ke kusa da su.
"Ka da a manta da katin asibitin yaron domin shi ne zai ba ma'aikatan lafiya damar gane inda aka tsaya da kuma sauran alluran da suka rage a yi wa yaron ko yarinyar."
Karin labaran da za ku so ku karanta
Hukumar ta kuma yi kira ga waɗanda ba su kai ƴaƴansu asibiti ba saboda bayyanar annobar korona:
"Duk wanda bai kai ɗansa asibiti ya karɓi allurar riga-kafi ba, ya sani ya saka shi cikin hatsari babba. Sai ya yi ƙoƙarin kai shi cibiya mafi kusa da shi domin akwai ma'aikatanmu a can suna aikin kula da lafiyar al'umma kamar yadda aka saba."
A halin da ake ciki, hukumar ta horas da kimanin ma'aikatan lafiya 250,000 da aka ɗora wa alhakin tabbatar da an yi wa waɗannan yaran da ba a yi wa allurar riga-kafin ba.
Ya kuma ce, "akwai ma'aikatan lafiya da ke aikin sa kai da ke cikin ƙauyuka da garuruwanmu, su ma mun ba su horo na musamman domin su riƙa faɗakar da al'umma cewa har yanzu fa ana bayar da riga-kafin nan fa a asibitocin da ke ƙananan hukumomi."
Tallafi daga hukumar lafiya ta duniya, WHO
Gabanin zuwan cutar korona a Najeriya, hukumomin kiwon lafiya musamman a matakin farko na samun tallafi daga hukumar WHO.
Amma abubuwa sun sauya tun bayan bayyanar cutar, kuma tallafin da hukumomi da ƙungiyoyi kan samar wa ƙasashe masu tasowa ya kusan tsayawa cik.
Dakta Adamu ya ce wannan koma baya ne amma duk da haka gwamnatin Najeriya ta ci gaba da sauke nauyin da ke kan ta na samar da ingantaccen kiwon lafiya.
"Gwamnati ta ci gaba da kayayyakin da ma'aikatan lafiya ke sanyawa domin kare kansu daga kamuwa da cututtuka masu yaɗuwa da sauran kayayyaki kamar magunguna".