Norwich na son sayar da Ben Godfrey kan £50m, Havertz yana son tafiya Chelsea

An wallafa

Norwich City tana son a biya ta kusan £50m kan dan wasan da ke tsaron baya Ben Godfrey, 22, a yayin da Borussia Dortmund da RB Leipzig suke zawarcin dan kwallon na Ingila da ke buga gasar Under-21. (Sky Sports)

Dan wasan Kai Havertz, mai shekara 21, ya shirya domin shigar da bukatar barinsa Bayer Leverkusen bayan ya shaida wa Chelsea cewa yana son komawa can a bazara. (Star)

Chelsea tana fatan yin amfani da damar sha'awar da Havertz ya nuna ta haduwa da 'yan kasarsa ta Jamus Timo Werner, mai shekara 24, da Antonio Rudiger, mai shekara 27, a Stamford Bridge. (Telegraph)

Wakilin Kevin de Bruyne ya yi watsi da maganganun da ake yi cewa dan wasan na Belgium mai shekara 29 yana shirin barin Manchester City domin komawa Real Madrid ko Paris St-Germain. (Sporza, via Star)

Ajax ta bi sahun Tottenham a yunkurin dauko dan wasan Southampton daDenmark, Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 24, yayin da ita ma Everton take son dauko dan wasan. (Telegraph)

Wakilin dan wasan Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 24, ya ce dan wasan na tsakiya bai kulla wata yarjejeniya da Manchester United ba inda kungiyarsa ta sanya farashin £80m a kansa. (Metro)

Tsohon abokin kwallon dan wasan Brentford da Algeria Said Benrahma, mai shekara 24, ya taya shi murnar komawa Chelsea a sakon da ya wallafa a Instagram - yana karin hasken cewa dan wasan ya amince da kwangila, wacce ta wuce £30m. (Sun)

Manchester City tana da kwarin gwiwar cewa dan wasan da ke tsaron baya Eric Garcia, dan shekara 19, zai ci gaba da zama a yayin da ake rade radin zai koma tsohuwar kungiyarsa Barcelona. (Manchester Evening News)

Juventus ta amince wa Chelsea ta zabi 'yan wasanta biyu, ciki har da dan wasan Wales Aaron Ramsey, mai shekara 29, domin ta karbo dan wasan Italiya Jorginho, mai shekara 28. (Express via Tuttosport)

Sevilla tana shirin dauko dan wasan Arsenal da Sufaniya Hector Bellerin, mai shekara 25, a bazarar nan. Juventus da Inter Milan su ma suna zawarcin dan wasan. (Express)

Manchester United na son dauko dan Bournemouth dan kasar Netherlands Nathan Ake, mai shekara 25,da dan wasan Aston Villa da Ingila Tyrone Mings, mai shekara 27 da na AC Milan da Italiya Alessio Romagnoli, 25, a matsayin wani zabi da ya rage mata kan Harry Maguire don cike gurbin tsakiya. (ESPN)

Sai dai kocin United Ole Gunnar Solskjaer ya nesanta kansa daga yunkurin dauko Ake da ma duk wani dan wasan tsakiya. (Metro)

RB Leipzig ta maye gurbin dan wasanta da zai koma Chelsea Timo Werner, mai shekara 24, da dan wasan Red Bull Salzburg da Koriya ta Kudu Hwang Hee-chan, mai shekara 24. Shi ma dan wasan Jamus Benjamin Henrichs, mai shekara 23, zai tafi zaman aro a RB Leipzig dagaMonaco.(ESPN)