Coronavirus a Afrika: Yawan masu korona ya haura 500,000 a Afrika

An wallafa

Yawan masu cutar korona ya haura 500,00 a Afrika a ranar Laraba, kuma ana fargabar yawan zai karu saboda yadda ake ci gaba da samun sabbin masu kamuwa da cutar a kasashen Afrika da dama.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, reshen Afrika ta fitar a ranar Laraba, inda ta kara da cewa cutar ta halaka mutum 11,959 cikin wata biyar a nahiyar, yawan da ya wuce na wadanda suka rasa ransu sakamakon cutar Ebola da aka yi fama da ita tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016 a yammacin Afrika.

Sanarwar ta kara da cewa yawan masu cutar ya rubanya a kasashe 22 da ke nahiyar cikin wata guda da ya gabata. Kusan kashi biyu cikin uku na kasashen na fuskantar ci gaba da yaduwarta ne a cikin al'umma.

Kasashen Aljeriya da Masar da Ghana da Najeriya da Afrika Ta Kudu ne ke da kashi 42 cikin 100 na masu dauke da cutar a Afrika, inda Afrika Ta Kudu kawai ke da kashi 29 cikin 100 na jumullar masu dauke da cutar a nahiyar.

Sannan kasashe irin su Gambiya, da Mali da Seychelles da Togo kuwa ba sa samun karuwar masu cutar sosai. Kasar Seychelles ba ta samu sabon wanda ya kamu da cutar ba kusan wata biyu amma a makon da ya gabata sai ta samu mutum 12 da suka kamu.

''Akwai alamu na samun ci gaba na yadda yaduwar cutar take raguwa a kasashe 10 cikin watan da ya gabata.

''Kashi 80 cikin 100 na masu kamuwa da cutar 'yan shekara 60 ne zuwa kasa, watakila saboda mafi yawan al'ummar Afrika matasa ne. Sai dai wadanda suka fi mutuwa sakamakon cutar 'yan shekara 60 ne zuwa sama,'' in ji sanarwar.

Daraktan WHO a Afrika Dakta Matshidiso Moeti ya ce: ''A yayin da kashi uku cikin hudu na kasashen Afrika ke samun karuwar masu dauke da cutar, tsarin kiwon lafiyar nahiya na fuskantar matukar barazana daga annobar Covid-19.''

A yayin da COVID-19 ke kara bazuwa a Afrika, dubban ma'aikatan lafiya sun kamu da cutar, don haka bai wa ma'aikatan lafiya kariya da wadata su da kayan aiki ya zama wajibi, in ji WHO.

"WHO tana aiki tukuru don taimaka wa ma'aikatan lafiya na Afrika da kayan aikin da suke bukata tare da ba su horo don rage barazanar da suke fuskanta.''