Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jair Bolsonaro: Shugaban ƙasar da ke ƙaryata korona ya kamu da ita
Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya kamu da cutar korona.
Wannan ne karo na hudu da aka yi masa gwajin, wanda aka yi masa a ranar Litinin bayan nuna alamun kamuwa da cutar ciki har da zafin jiki.
Mista Bolsonaro ya sha nuna wannan cutar ba wata aba ba ce, yana kiranta 'yar karamar mura yana kuma cewa ba za ta taɓa kwantar da shi ba.
Ya kuma umarci gwamnonin yanki da su sassauta dokar kullen da aka sanya saboda shawo kan annobar korona, wanda ya ce tana hana ci gaban tattalin arziki, a ranar Litinin ne kuma ya sassauta dokar sanya takunkumi.
Idan muka koma watan Afirilu, ya ce idan cutar ta kama shi ba zai damu kanshi ba saboda ba zai ji komai ba, ''abin da zan iya ji shi ne kamar wata 'yar mura nake.''
Lokacin da ya yi wannan maganar, mutanen da cutar ta kashe ba su fi 3,000 ba a kasar, kuma 40,000 ne suka kamu duka.
Amma tun daga nan cutar take ta bazuwa kamar wutar daji. Ya zuwa ranar Litinin adadin mutanan da suka mutu ya kai 65,000 wadanda suka kamu kuma sun kai miliyan daya da dubu dari shida, kasa ta biyu kenan bayan Amurka.
Duk da karuwar masu cutar, Shugaba Bolsonaro ya ta yin musun illar da dokar kulle ke yi ta fi ta cutar korona ita kanta, ya kuma zargi kafafen yada labarai da tsorata mutane.
Jair Bolsonaro kan annobar korona:
- "Daga abin da na gani har zuwa yanzu, akwai wasu nau'ukan mura da suka fi korona hadari" (11 Maris)
- "A yau muna da labari, saboda muna da yanayi mai zafi a Brazil mun kusa ganin karshen wannan annoba, ko ma in ce mun wuce(...) cutar ba ta yaduwa a wurare masu zafi kamar na mu" (18 Maris)