Coronavirus: Ana fargabar yaɗuwar cututtuka daga dabbobi zuwa mutane

An wallafa

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa cutukan da ke yaɗuwa daga dabbobi zuwa mutane na ci gaba da karuwa, kuma za a cigaba da fuskantar hakan matsawar ba a ɗauki matakin kare dabbobi da kuma gandun daji ba.

An ɗora laifin cututtukan masu yaɗuwa kamar cutar korona kan yadda ake yawan dogaro da samun sinadari mai gina jiki daga dabbobi da ayyukan noma da kuma sauyin yanayi.

Rahoton hukumar bincike kan muhalli ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya gano cewa a duk shekara irin wadannan cutuka da dabbobi ke shafawa mutane na kashe mutun miliyan biyu a duk shekara.

Sannan annobar korona za ta janyo mummunan hasara ga tattalin arzikin duniya dala tiliyan tara tsawon shekaru biyu.

Cutar Ebola da Sars har ma da cutar Korona dukkaninsu daga dabbobi suka yaɗu zuwa ga mutane.

Me rahoton ya ce?

Rahoton ya ce ƙaruwar ba kai tsaye ba ne, ya faru ne daga lalacewar muhalli - misali ta hanyar lalacewar ƙasa da farautar dabbobi da haƙar albarkatun ƙasa da kuma sauyin yanayi wanda ya sauya yada dabbobi ke mu'amula da mutane.

"A cikin ƙarni daya an samu aƙalla annoba sau shida na naurin korona," a cewar Inger Anderson, shugabar hukumar kare muhalli ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

"A shekaru 20 da suka gabata, kuma kafin ɓarkewar annobar korona, cututtukan da ake samu daga dabbobi sun janyo hasarar dala biliyan 100.

Ta ce mutum miliyan biyu ke mutuwa duk shekara a ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi da matsakaita daga cututtukan da dabbobi ke shafawa mutane da ba a damu da su ba.

"Wannan ya shafi al'umomin da ke tattare da matsaloli na ci gaban rayuwa da kuma dogaron da suke da dabbobi da kusanci da namun daji."

Buƙatar nama, misali ya karu da kashi 260 a shekaru 50, inji Ms Andersen.

Ta ƙara da cewa mun ƙara inganta harakar noma, da faɗaɗa abubuwan more rayuwa haƙar ma'adinan ƙarkashin kasa a dazuka.

Madatsun ruwa da noman rani da gonaki na da alaƙa da kashi 25 na cuttukan da ke yaɗuwa ga mutane. Tafiye tafiye da sufuri da hanyoyin samar da abinci sun tayar da kan iyakoki da tazara. Sauyin yanayi ya taimaka ga yaɗuwar kwayoyin cuta.

Rahoton ya ba gwamnatoci shawarwri kan yadda za su ɗauki matakan kaucewa sake ɓarkewar wata annoba nan gaba, kamar kula da ƙasa da kashe kuɗi domin gudanar da binciken kimiya.

"Ilimin kimiyya ya fayyace cewa idan muka ci gaba da farautar namun daji da lalata muhallinmu, to za mu ci gaba da fuskantar wadannan annoba da ke yaɗuwa daga dabbobi zuwa ga mutane a tsawon shekaru masu zuwa," inji Andersen

Ilimin kimiyya ya bayyana a sarari cewa idan muka ci gaba da amfani da dabbobin daji da lalata muhalli, to za mu iya tsammanin ganin kwararar wadannan cututtukan suna tsalle daga dabbobi zuwa ga mutane a shekaru masu zuwa, "in ji Ms Andersen.