Coronavirus a Najeriya: Ƙauyen da ba su san da cutar korona ba a Abuja

Zokutu women
    • Marubuci, Dooshima Abu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin, Abuja
  • An wallafa

Duk da irin dumbin kudaden da gwamnatin Najeriya ke amfani da su wajen wayar da kai kan yaduwar cutar korona, har yanzu akwai wasu yankuna a kasar da ba su san komai game da cutar mai kisa ba.

Ƙauyen Zokutu na da nisan tafiyar sa'a biyu daga Abuja, babban binin kasar, inda a nan ne kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar korona yake fitar da bayanai a kullum game da cutar.

Amma mazauna yankin sun ce ba su taba jin labarin annobar korona ba da kuma bayani kan yadda za ta iya shafar su.

An shafe tsawon sama da kwana 100 da Najeriya ta samu mutum na farko mai dauke da cutar, kuma a yanzu korona na ci gaba da yaduwa, sannan yawan masu dauke da ita ma na karuwa duk rana.

Alƙaluman hukuma dai sun nuna cewa fiye da mutum 20,000 ne zuwa yanzu suka kamu da cutar, wadda kuma ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 500 a Najeriya.

Daga cikin manyan hanyoyin da gwamnati ke bi wajen yada bayanai ga jama'a sun hada da hanyar rediyo da talabijin da shafukan sada zumunta.

Amma ƙauyen Zokutu ba su da titin mota mai kyau, ba su da asibiti sannan ba su da hanyoyin sadarwa na zamani.

Haka kuma, ba su da wutar lantarkin da za su kunna rediyo ko talabijin don jin labarai kan abin da ya shafi cutar korona, don haka ba sa samun labari kan duk wani mataki da gwamnati ke dauka.

Rose Mishayi
Bayanan hoto, Rose Mishayi ta ce ba ta san komai kan wannan cutar ba

Wata mazauniyar garin Rose Mishayi, ta ce ba mu samu labarin ba sam.

''Wannan cutar ta korona ba mu taba jin komai a kanta ba. A yanzu haka dai mu ba mu ma san ta yadda cutar za ta iya kama mu ba.

''Mun dai ji labarin wai wata cutar korona ta shigo Najeriya amma ba mu san komai a kanta,'' in ji Mishayi.

Woman dey fetch water for stream
Bayanan hoto, Ƙauyen Zokutu ba su da ruwan sha mai kyau

Tun bayan bullar cutar dai gwamnati take ta umartar mutane da su dinga sa takunkumi, da wanke hannu da yin nesa-nesa da juna.

Amma a lokacin da sashen BBC Pidgin ya kai ziyara kauyen, mutane suna ta hidimominsu ba tare da damuwa da saka takunkumin ko bin dokar yin nesa-nesa da juna ba.

Zokuto villagers dey fetch water for stream
Bayanan hoto, Mafi yawan mazauna kauyen noma ce sana'arsu

Hajara Solomon ta ce ba su taba samun wani bayani kan dokar nesa-nesa da juna ba.

''Idan wannan cutar ta kama wani a yanzu, babu wani asibiti da za a iya kai mutum a nan, sai dai a kais hi asibitin koyarwa na Gwagwalada, idan kuma ba ka da kudi sai da ka sha wahala ka mutu.

"Gwamnati ba ta tunawa da mu sai a lokacin yakin neman zabe, da zarar an gama zabe kuma sai su tafi su manta da mu,'' in ji Solomon.

Solomon ya ce idan haka ne, yanzu su da ke cikin duhun kan wannan cutar, su ne suka fi fuskantar barazanar kamuwa da ita kenan.

Zoktutu village
Bayanan hoto, Tafiyar sa'a biyu ce zuwa kauyen Zotutu daga Abuja

Ministan yada labarai Lai Muhammed ya ce gwamnati ta zuba kudi sosai wajen yin sanarwa a gidajen talabijin da rediyo don ilimantar da 'yan Najeriya kan cutar korona.

A cewarsa, wata kuri'ar jin ra'ayin mutane da aka yi ta nuna cewa kashi 99 cikin 100 na 'yan kasar sun ji labarin cutar.

Amma kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona ya ce mutane na bukatar jin labarin cutar nan musamman a yanzu da take shiga cikin al'umma sosai.

Wata hukuma ta gwamnatin ce take daukar nauyin koyar da 'yan kasar tare da ba su bayanai kan tsare-tsaren gwamnati.

Duk da cewa hukumar ta cetana kokari sosai wajen ilimantar da 'yan Najeriya kan wannan cuta, to al'ummar kauyen Zokutu dai ba su san da hakan ba duk d acewa suna makwabtaka da Abuja.