Coronavirus a Afirka: Cutar 'na yaɗuwa cikin gaggawa' a nahiyar

An wallafa

Annobar cutar korona na ƙara hauhawa cikin sauri a Nahiyar Afirka, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Shugaban hukumar ta yankin Afirka, Matshidiso Moeti, ta ce yanzu cutar na fantsama ne a wajen birane kuma rashin kyawawan kayayyakin gwaji na ƙara daƙile yadda ake tunkararta.

Ya zuwa yanzu, Nahiyar Afirka ce wadda annobar ba ta yi wa mummunan kamu ba.

Afirka ta Kudu na da fiye da kashi ɗaya cikin huɗu na waɗanda suka kamu da cutar sannan kuma annobar a yankin Western Cape na ƙasar na kama da wadda ake gani yanzu a Nahiyar Turai.

Cibiyoyin harkokin lafiya a Afirka ta Kudu na daga cikin mafiya kyawu a Afirka, sai dai akwai fargabar cewa ƙaruwar masu kamuwa da cutar cikin sauri ka iya fin ƙarfinta.

A jumlace, akwai fiye da mutum miliyan 7.3 da suka harbu da korona a duniya kuma sama da 416,000 sun rasa rayukansu.

Dr Moeti ta faɗa wa wani taron WHO a Geneva cewa Afirka na da mutum kusan 200,000 da suka harbu da cutar sai kuma 5,000 da suka mutu, yayin da ƙasa 10 ke da kashi 75% na waɗanda suka kamun.

Ta ce akwai yiwuwar a ci gaba da samun masu ɗauke da ita nan gaba kaɗan.

"Daga yanzu zuwa lokacin da muka samu riga-kafi, ina ganin sai dai mu ci gaba da fuskantar ƙaruwar yaɗuwarta a yankin, yayin da wasu ƙasashe ke samun gari guda cike da masu cutar da yawa kamar a Afirka ta Kudu da Aljeriya da Kamaru, waɗanda suke buƙatar ƙwararan matakan lafiya irin su nesa-nesa da juna," in ji ta.