Makiyayan kasashen Afirka ne ke shigo da makamai - Ganduje

Gwamna Ganduje

Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

An wallafa

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga gwamnatin Tarayya ta hana makiyaya daga kasashen Afirka tsallakowa Najeriya domin magance matsalar rikicin makiyaya da manoma.

Gwamnan na Kano wanda ya yi kiran yayin kaddamar gidaje 25 karkashin shirin tsugunar da makiyaya da ake kira RUGA a karamar hukumar Kiru, ya yi zargin cewa makiyaya da ke tsallakowa daga kasashen Afirka ke shigo da makamai a Najeriya.

A sanarwar da sakataren yada labarai na gwamnan ya fitar Abba Anwar, gwamna Ganduje ya ce: "yadda suke shigo da makamai ne ya kara rura wutar rikici tsakanin makiyaya da manoma."

"Kiran ya zama dole domin a hana makiyaya shigowa daga wasu kasashen Afirka." in ji shi.

Gwamnan ya kara da cewa yadda makiyayan ke kwarara ne ya kara haifar da rikic tsakanin makiyaya da sauran kabilu baya ga manoma.

Gwamna Ganguje ya ce manufar samar da matsuguni ga makiyaya shi ne, hana su yawo wanda shi ne dalilin ikici tsakaninsu da manoma da kuma kawo karshen satar shanu.

A cewar gwamnan samar da matsuguni ga makiyaya shi zai kawo karshen satar shanu da garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

fulani Makiyaya

Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

Gwamna Ganduje ya kuma ce shirin na ruga a Kano ba iya fulani makiyaya da ke jihar kawai ne za su amfana ba, inda ya yi kira ga makiyaya na sauran jahohin Najeriya su shigo jiharsa ta Kano.

Batun tsugunar da Fulani wuri guda dai ya haifar ce-ce-ku-ce a Najeriya inda wasu da suka hada har da makiyaya ke sukar shirin, wasu ke ganin shi ne tsarin da ya fi dacewa da zai kawo karshen rikicin makiyaya da manoma wanda yanzu ya rikide ya koma hare-haren 'yan bindiga da satar mutane domin kudin fansa.Wasu makiyayan sun fi son a bar su su ci gaba da yawo da shanunsu maimakon tsugunar da su da gwamnati ke shirin yi.