Zan yi addu'ar Allah Ya saka min - Aminu Babba Ɗan'agundi

Bayanan sautiMuryar Aminu Babban Dan'agundi
An wallafa

Latsa alamar lasifika da ke sama don sauraren hira da Aminu Babban Ɗan'agundi:

Aminu Babban Ɗan'agundi, mutumin da Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da matakin da marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya dauka na tube rawaninsa shekara 17 da suka gabata, ya ce zai ci gaba da addu'ar Allah Ya saka masa kan zaluncin da ya ce an yi masa.

A hirar da ya yi da BBC bayan hukuncin Kotun Kolin, tsohon basaraken ya ce ko da yake ya karbi hukuncin a matsayin nufin Allah, amma bai taba tunanin za a ba shi rashin nasara ba ganin cewa kotunan da ya je a baya duk sun ba shi nasara.

"Na karbi [hukuncin] ba ni da wani ja a kai; kuma duk wanda yake ganin ko ya yi wani abu a kai, na bar shi da Allah. Da ma hakkina na tafi nema kuma har yanzu ina nan zan gaya wa Allah Ya yi min sakayya," in ji shi.

Ya kara da cewa lokacin da aka cire shi daga sarautar ya yi matukar bakin ciki amma yanzu yana jin dadi "domin da ba a cire ni ba da Allah bai min suturar da ya yi min a yanzu ba."

Ranar Juma'a ne Mai shari`a Mary Odili ta Kotun Kolin Najeriya, ta jagoranci alkalan Kotun su biyar wajen tabbatar da matakin da marigayi Ado Bayero ya dauka na cire Aminu Babban Ɗan'agundi daga mukaminsa na Sarkin Dawaki Maituta kuma hakimin Gabasawa.

A shekara ta 2003 ne marigayi mai martaba Sarkin Kano Ado Bayero ya sauke Aminu Babba Dan`agundi daga mukamin nasa, bayan an zarge shi da nuna rashin da`a ga sarki, da aikata wasu laifuka da suka saba da dabi`un mai rike da mukami irin nasa.

Cikin dabi'un har da korafin da aka ce al`umar masarautarsa ta rubuta a kansa, tana zarginsa da shiga harkar siyasa da shirya magudi, a zaben da aka yi a shekera ta 2003. Amma ya musanta.

Daga nan ne Aminu Babba Dan`agundi ya kai kara wata babbar kotu a Kano, inda ya kalubalanci Sarki da fadar Kano dangane da tube masa rawani da aka yi masa, musamman ma huruminta na yin hakan, inda alkalin kotun mai shara`a Muhammad Sadi Mato ya ba shi gaskiya, kana ya umurci fadar Kano ta mayar da shi kan mukaminsa, tare da biyansa dukkan hakokinsa.

Sai dai fadar sarkin Kano ta kai kara gaban wata kotun daukaka kara, wadda ita ma ta sake ba wa Aminu Babba Dan`agundi gaskiya.

A can ma, fadar Sarkin Kanon ba ta daddara ba, sai ta wuce Kotun Koli, wadda a karshe Kotun Kolin ta amince da bukatarta ta tabbatar da matakin da marigayi Sarki Ado Bayero ya dauka na sauke shi daga mukamin nasa.

Gabannin wannan hukunci na Kotun Kolin Najeriyar, kusan shekara 17 aka shafe ana tabka wannan shari`ar.

Wannan shari`a tsakanin Aminu Babba Dan`agundi da marigayi mai martaba Sarki Ado Bayero ta ja hankali sosai kasancewar wannan ne karon farko da hakimi ko dan majalisar nadin sarkin Kano ya kai karar sarki a kotu.