Shafin Twitter ya zargi Trump da shirga ƙarya

Kamfanin Twitter ya zargi shugaban Amurka Donald Trump da yin karya, a daya daga cikin labaran da shafin ya wallafa.
Matakin - wanda ya zargi shugaban da yin karya - yana kunshe ne a sakon Twitter da Mr Trump ya wallafa game da tsohon Sakataren tsaronsa.
Mr Trump ya wallafa sakon Twitter cewa shi ya sanya wa James Mattis sunan "Mahaukacin kare" sannan daga baya ya kore shi daga aiki.
Sakon na Twitter ya ce tsohon Sakataren Tsaron na Amurka ya sauka daga mukaminsa, kuma tun kafin Trump ya hau mulki aka sanya masa sunan "Mahaukacin kare".
Hakan ya faru ne bayan a makon jiya Twitter ya sanya wata alama ta duba sahihancin wasu sakonni da Shugaba Trump ya wallafa, sannan ya ce shugaban yana goyon bayan tashin hankali.
Twitter ya dauki matakin ne kwana guda bayan James Mattis ya soki shugaban ƙasar da cewa yana jawo rarrabuwar kawunan mutane da gangan musamman game da yadda yake daukar mataki bayan kisan wani bakar fata, George Floyd, a hannun 'yan sandan Amurka.
Ya ce ya ji taƙaici kan yadda Mista Trump ke yi wa lamarin zanga-zangar da ake yi kan kisan Mr George Floyd riƙon sakainar kashi.

Asalin hoton, Twitter
"Donald Trump ne shugaban ƙasa na farko a tsawon rayuwata da ba ya ƙoƙarin haɗa kan Amurkawa - kuma ba ya ko ƙoƙarin gwadawa," Mista Mattis ya rubuta a mujallar The Atlantic. "A maimakon haka sai yake ƙoƙarin raba kawunanmu."
Ya ci gaba da cewa: ''Muna kallon yadda sakamakon abubuwan da aka shafe shekara uku ana yi da gangan ke kasancewa. Muna kallon sakamakon abin da yake faruwa a shekara uku na rashin shugabanci nagari.''









