Trump zai ɗauki 'ƙwaƙƙwaran mataki' kan shafukan sada zumunta

Donald Trump

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Laraba ne Shugaba Trump ya soki Twitter da hana shi 'yancin fadin albarkacin baki bayan a karon farko shafin ya bayyana wani sako da shugaban ya wallafa a matsayin na yaudara
An wallafa

Ana sa ran Shugaban Amurka Donald Trump zai sanya hannu kan dokar shugaban kasa ta musamman da za ta sauya fasalin dokokin da ke kare shafukan sada zumunta.

Hakan na nufin za a iya yin karar shafuka irin su Facebook da Twitter idan har kotu ta same su da laifin toshe sakonnin mutane ta hanyar yaudara.

Daftarin na dokar shugaban kasar ta musamman ta ce shafukan sada zumunta na nuna son kai wajen tace bayanai.

Mr Trump yana yawon sukar shafukan sada zumunta kan nuna wariya wajen bayanan da suke tacewa.

A ranar Laraba ne Shugaba Trump ya soki Twitter da hana shi 'yancin fadin albarkacin baki bayan a karon farko shafin ya bayyana wani sako da shugaban ya wallafa a matsayin na yaudara.

''Ƙwaƙƙwaran mataki zai biyo baya,'' kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Me dokar shugaban kasar ta ce?

Dokar za ta fayyace dokar Amurka da ta bai wa shafukan sada zumunta kariya a wasu yanayin.

Karkashin sashe na 230 na dokar, ba a kama shafukan sada zumunta da laifin da masu amfani da su suka wallafa, amma za su iya toshewa ko cire sakon da ke da tayar da hankali ko harzuka.

Me shafukan sada zumuntar suka ce?

Twitter, wacce aka yi ta ambatonta a daftarin dokar ta ki cewa komai.

YouTube ma wanda mallakin kamfanin Google ne bai ce komai ba.

A wata hira da tashar Fox News ta yi a ranar Laraba da shugaban Facebook Mark Zuckerberg, ya ce sanya ido kan shafukan sada zumunta ba shi ne mafita ba daga gwamnatin da ke rajin kare hakan.