Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Ma'aikatan lafiya 812 ne suka kamu da korona a Nigeria
Adadin ma'aikatan lafiya da suka harbu da cutar korona ya ƙaru zuwa 812, a cewar Dr. Chikwe Ihekweazu, Shugaban Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya.
Shugaban NCDC ya faɗi hakan ne ranar Talata a wurin taron manema labarai na kullum da kwamitin shugaban ƙasa kan yaƙi da annobar korona ke yi a Abuja.
Ya bayyana cewa 29 daga cikinsu ma'aikatan hukumar NCDC ne da suka kamu da cutar yayin ayyukan kula da masu jinyarta.
"Mun samu 812 ma'aikatan lafiya da suka kamu da cutar korona," in ji shi.
Ya ci gaba da cewa: "Ba wai adadinsu ba kawai; 29 daga ciki ma'aikatan NCDC ne. Mutane ne da na sani kuma suna da iyali; mata da ƙananan yara."
Kazalika ya yi magana kan ci gaban da aka samu zuwa yanzu game da yaƙi da annobar a Najeriya, inda ya tabbatar da cewa fiye da mutum 10,000 sun kamu da ita.
A cewarsa, kashi 60 cikin 100 na mutanen suna ƙananan hukumomi 20 a faɗin Najeriya.
"An ƙara ƙarfafa yadda ake kare jama'a daga cutar, yayin da a lokaci guda kuma ake sassauta dokokin kulle.
"Zarce 10,000 da adadin waɗanda suka kamu suka yi muhimmin abu ne kuma duk sanda muka bayar da lissafinsu sai ku ji su da yawa. Sai dai kuna mantawa cewa mutane ne [ba lamba ba]."
Alƙaluma daga NCDC sun nuna cewa mutum 65,885 aka yi wa gwajin cutar a Najeriya, 10,819 daga cikinsu sun kamu da ita sannan 314 suka mutu, sai kuma 3,239 da suka warke.