A.A. Sule: Yadda jihar Nasarawa take ɗawainiya da ƙananan hukumomi

Nasarawa State Governor AA Sule
Bayanan hoto, Gwamna A.A. Sule na jihar Nasarawa
    • Marubuci, Haruna Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
  • An wallafa

A cikin shirin 'A Fada a Cika' wanda BBC Hausa ke shiryawa, gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya ce wata hudu bayan hawan sa mulki ne kananan hukumomin jihar suka koka kan cewa ba za su iya biyan cikakken kudin albashin ma'aikatansu ba.

A cewarsa: "Daga cikin kudin jiha nake cirewa ina taimaka masu suna biyan cikakken kudin albashi da kuma fansho har zuwa wata uku."

Tun farko dai wata mai suna Rukayya Basha daga Keffi ta turo tambaya ta faifan bidiyo, inda tace:

"Gwamna ka yi alkawari cewa idan ka hau mulki za ka rika biyan mutane full salary (Cikakken albashi), saboda gwamnatin da ta gabata tana biyan mutane albashi rabi da rabi, amma kai kuma ka yi alkawarin cewa ko bashi za ka iya ciyowa saboda ka ga cewa ka biya mutane.

Ta ci gaba da cewa, "To amma kuma ga shi tun gwamnatin naka ba ta je ko ina ba ka fara biyan mutane cikin percentage (wani bari na albashi). To ko me ya sa haka? Bashin ne ba ka ciyo ba koko mene ne ke faruwa?"

Wasu 'yan jihar Nasarawa da suka sami shiga shirin 'A fada a cika' na BBC Hausa
Bayanan hoto, Wasu 'yan jihar Nasarawa da suka sami shiga shirin 'A Fada a Cika' na BBC Hausa

Sai dai gomman kananan hukumomi ne ke biyan wani bangare na albashin ma'aikata a karshen wata, ba gwamnatin jiha ba.

Ya ce daga watan uku ne ita ma gwamnatin jihar ta lura cewa ba za ta iya ci gaba da tallafa wa kananan hukumomin ba. Tun daga wannan lokacin ne kananan hukumomi suke biyan ma'aikatansu kashi 70 cikin 100 na albashinsu a kowane wata.

A shekarar ta 2019, kafin hawansa kan mukamin gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule ya yi alkawari a lokacin wata muhawara da BBC ta shirya cewa idan ya hau mulki zai rinka biyan ma'aikata albashinsu a kammale.

Ya ce "Babu shakka daga zuwa ko bashi za mu yi, za mu ci domin mu biya ma'aikata hakkinsu."

Gwamnatin da ta gabata a jihar a wadansu lokutan ta rinka biyan wani bangare ne na albashin ma'aikata, abin da a cewar gwamnan ya faru ne saboda raguwar kudaden shiga da take samu, musamman a sanadiyyar faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya.

Gwamna Abdullahi Sule yana muhawara da wasu 'yan jihar Nasarawa
Bayanan hoto, Gwamna Abdullahi Sule yayin muhawarar da BBC ta shirya da wasu 'yan jihar Nasarawa

Sai dai gwamnan ya ce tun da ya hau mulki gwamnatinsa ba ta gaza ba wajen biyan ma'aikata da ke karkashin gwamnatin jihar cikakken albashinsu.

"Tun da na hau mulki, har zuwa wannan wata na biyar, shekara daya cak, ko wane wata ana biyan ma'aikata kudinsu na cikakken kashi 100. Babu mutum daya da gwamnatina ta taba biya percentage'

A lokacin tattaunawar, wadda aka yi ta amfani da fasahar sadarwa ta 'Zoom', al'ummar jihar Nassarawa wadanda suka samu shiga shirin sun yi tambayoyi ga gwamnan kai-tsaye.

Wasu daga cikin abubuwan da suka yi tambayoyi a kai sun hada da tsaro, da noma, da tattalin arziki, da sauran su.

A bangaren tsaro wata mai suna Zainab M. Alhassan ta turo da sako a shafin BBC Hausa Facebook, inda ta ce:

"Kira na gare shi (gwamna). Don Allah ya dage, in ba haka ba jihar Nasarawa za ta dawo (kamar) dajin Sambisa. Toto local govt na cikin tashin hankali, har da wadansu kauyuka da ke kusa da Nassarawa local govt."

A lokacin da aka karanta masa wannan sako gwamnan ya ce gwamnatinsa ta dauki nauyin samar da wasu sansanonin sojoji da ake kira 'Military Super Camps' a Toto da Doma, da kuma Nassarawa.

Haruna Ibrahim Kakangi yana jagorantar shirin 'A Fada a Cika ta na'urar zamani ta Zoom
Bayanan hoto, Haruna Ibrahim Kakangi yana jagorantar shirin 'A Fada a Cika' ta na'urar zamani ta Zoom

Sannan gwamnatin jihar ta dauki matakai wajen shawo kan matsalar tsaron da ake fuskanta a yankin na Toto, ta hanyar gudanar da aikin hadin guiwa tsakanin sojin sama da na kasa da kuma 'yan sanda domin kawar da wasu masu aikata laifi da suka yi sansani a yankin.

Sai kuma wata tawagar rundunar 'yan sandar kwantar da tarzoma da aka kai garin Toto, duk domin tabbatar da tsaro, yayin da kuma gwamnati ke samar da ayyukan yi ga matasa domin rage matsalar.

Ya kuma ce a farkon mulkinsa ya gana da gwamnan jihar Benue inda suka tattauna kan hanyoyin da za a magance matsalar tsaro.

Baya ga haka an yi tambayoyi a kan aikin noma da kuma hako ma'adanai, sannan tun a farko gwamnan ya yi bayani kan matakan da jihar ta dauka na yaki da cutar korona.

Ya ce an dauki matakai irin na hana zirga-zirga da kuma yin gwaji ga wadanda ake zargin suna dauke da cutar.