Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus a Najeriya: Masu korona sun kai 7, 839, 226 sun mutu
Mutum 313 sun sake kamuwa da cutar korona a Najeriya a cewar alƙaluman hukumar daƙile cutuka masu yaduwa ta ƙasar. Ɗaukacin masu cutar ya kai 7,839.
Sai dai, daidai lokacin da ake ƙara samun adadin mutanen da cutar ke ƙara harba, haka kuma mutanen da suke warkewa su ma suna ƙaruwa. Yanzu dai mutum 2,263 ne aka tabbatar sun warke a Najeriya.
Kusan rabin mutanen da suka sake kamuwa da koronan suna Lagos, jihar da ta fi fama da annobar a Najeriya. Yanzu dai tana da masu cutar 3,505.
Jihar Kano ita ce ta biyu da yawan masu korona 896, sai Abuja na Uku da yawan masu korona 505. Haka zalika, an ba da rahoton samun ƙarin mutum shida da cutar ta harba a jihar Filato.
Sauran Jihohin da aka samu sabbin kamu akwai Rivers da ke da mutum 27, sai Edo mai mutum 19.
Kano an samu mutum 13 bayan jadawalin jiya Asabar ya nuna babu mutum ko guda da aka samu wanda ya harbu da cutar.
Ogun na da mutum 12, yayinda Ebonyi ke da 11.
Ita ma Nasarasawa da kuma Jihar Delta an samu mutum 8, 8 a kowacce jiha.
Masu cutar a jihohin Oyo sun karu da 6, Kaduna kuwa mutum 5, kwara mutum 4.
Akwa Ibom da Bayelsa Mutum uku-uku. Sai Nijar da Anambra mutum 1, 1.
Har yanzu a hukumance cutar korona ba ta ɓulla cikin jihohin Kogi da Cross river ba, amma wasu na cewa mai yiwuwa akwai annobar cikinsu, kawai dai don ba a yin gwaji ne.
Muhimman bayanai kan annobar korona
An fara gano cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.
Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an sallame su daga asibiti.
A ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin korona a kasar.
Gwamnoni irinsu Bala Mohammed da Nasir El-rufa'i da kuma Seyi Makinde na jihar Oyo duk sun kamu da annobar kafin su warke daga bisani.
Har yanzu a hukumance ba a samu bullar cutar a jihohin Kogi da Cross river ba, amma wasu na da ra'ayin cewa hakan ta faru ne saboda ba a gwajin cutar a cikin johohin biyu.
Hukumomin Najeriya dai sun ce sun rubanya adadin gwaje-gwajen da suke yi a kasar, inda a yanzu suka ce akan yi gwaji kimanin dubu guda cikin sa'a 24.
Ga jerin bayanan jihohin da korona ta bulla cikinsu ya zuwa daren Lahadi 24 ga watan Mayu.