Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Mutum miliyan 60 za su fada talauci a duniya
Shugaban Babban Bankin Duniya ya yi gargadin cewa mutum kusan miliyan 60 ne cutar korona za ta jefa cikin "matsanancin talauci".
David Malpass ya ce bankin na sa rai tattalin arzikin duniya zai janye da kashi 5 cikin 100 a wannan shekarar yayin da kasashe ke fama da annobar.
Dama dai wannan ya yi sanadiyyar miliyoyin mutane su rasa ayyukansu da durkushewar sana'o'I inda kasashe masu fama da talauci suka fi shiga mawuyacin hali.
"Miliyoyin ayyuka ne suka watse kuma ma'aikatun lafiya na cikin matsi a fadin duniya," a cewarsa.
"Kiyasinmu shi ne mutum miliyan 60 na iya shiga matsanancin talauci - wannan ya mayar da hannun agogo baya kan ci gaban da aka samu dangane da kawar da talauci a shekaru ukun da suka gaba," Mista Malpass ya yi gargadi ran talata.
Babban Bankin Duniya ya bayyana "matsanancin talauci" a matsayin mutum daya da ya dogara da kasa da dala 1.90 ko fam 1.55 a kowace rana.
Bankin da ke da ofishinsa a birnin Washington zai bai wa kasashe masu fama da talauci bashi da kyauta kudi dala biliyan 160 don shawo kan matsala. Mista Maples ya ce kasashe 100, da ke da kashi 70 cikin 100 na mutanen duniya ne aka bai wa kudin na taimakon gaggawa.
"Yayin da Babban Bankin Duniya ke samar da hanyoyin rage radadi, ba za su isa ba" a cewarsa.
Mista Malpass ya ce ya damu da yadda kananan bankuna ke jan kafa wajen bai wa kasashen bashi.
"Ban ji dadin yadda ake jan kafa ba. Har yanzu bankuna na karbar kudi daga kasashe masu fama da talauci kuma ya kamata su kara kaimi."
Babban Bankin Duniya ya yi aiki da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) a wani shiri na bai wa kasashe masu fama da talauci damar neman sassauci a biyan bashin da suka karba daga kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 har zuwa karshen wannan shekarar.
A lokaci guda, Jamie Dimon, Shugaban Bankin JP Morgan ya ce lallai ne annobar cutar korona ta zama izina wajen gina al'umma mai adalci.
"Babban fatana shi ne mu yi amfani da wannan annobar mu sake gina tattalin arziki da zai samar da dama mai dorewa ga mutane masu dumbin yawa, musamman wadanda aka baro a baya tun da dadewa," kamar yadda ya rubuta gabanin taron shekar-shekara na masu zuba jari a bankin ranar Talata.