Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus a Najeriya: Masu korona 167 sun warke Jajiberen Sallah
Mutum 265 sun sake kamuwa da cutar korona a Najeriya a cewar alƙaluman hukumar daƙile cutuka masu yaduwa ta ƙasar. Ɗaukacin masu cutar ya kai 7,526.
Sai dai, daidai lokacin da ake ƙara samun adadin mutanen da cutar ke ƙara harba, haka kuma mutanen da suke warkewa su ma suna ƙaruwa. Yanzu dai mutum 2,174 ne aka tabbatar sun warke a Najeriya.
Bayan hukumar NCDC ta ba da rahoton cewa marasa lafiya 167 sun warke kuma an sallame su daga cibiyoyin kwantar da masu korona ranar Asabar.
Haka kuma, alƙaluman sun ce babu ko mutum guda da ya rasu ranar saboda cutar ta korona a Najeriya.
Fiye da rabin mutanen da suka sake kamuwa da koronan suna Lagos, jihar da ta fi fama da annobar a Najeriya. Yanzu dai tana da masu cutar 3,357.
A wannan karo an samu kaso mai yawa na ƙarin masu cutar a jihohin Oyo da Ogun shiyyar kudu masu yamma, inda mutum 34 suka sake kamuwa a Oyo, Ogun kuwa mutum 23.
Ita ma jihar Edo, an samu sabbin masu cutar 28, yayin da babban birnin tarayya Abuja, aka ba da rahoton mutum 22 sun ƙaru.
Yanzu yawan masu korona a Abuja 469, ita ce ta biyu a yawan masu cutar a arewacin Najeriya. Haka zalika, an ba da rahoton samun ƙarin mutum shida da cutar ta harba a jihar Filato.
Sai Kaduna mutum biyar, Borno da Neja mutum uku kowaccensu.
Jihohin Kwara da Bauchi da Anambra da Enugu, NCDC ta ce mutum bi-biyu ne suka sake kamuwa da korona ranar Asabar
Har yanzu a hukumance cutar korona ba ta ɓulla cikin jihohin Kogi da Cross river ba, amma wasu na cewa mai yiwuwa akwai annobar cikinsu, kawai dai don ba a yin gwaji ne.
Muhimman bayanai kan annobar korona
An fara gano cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.
Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an sallame su daga asibiti.
A ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin korona a kasar.
Gwamnoni irinsu Bala Mohammed da Nasir El-rufa'i da kuma Seyi Makinde na jihar Oyo duk sun kamu da annobar kafin su warke daga bisani.
Har yanzu a hukumance ba a samu bullar cutar a jihohin Kogi da Cross river ba, amma wasu na da ra'ayin cewa hakan ta faru ne saboda ba a gwajin cutar a cikin johohin biyu.
Hukumomin Najeriya dai sun ce sun rubanya adadin gwaje-gwajen da suke yi a kasar, inda a yanzu suka ce akan yi gwaji kimanin dubu guda cikin sa'a 24.
Ga jerin bayanan jihohin da korona ta bulla cikinsu ya zuwa daren Asabar 23 ga watan Mayu.