Mun gode Allah Sarkin Daura ya samu lafiya- Buhari

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce yana cike da farin cikin bisa samun lafiya da Sarkin Daura, Umar Farouk ya yi.

A wani sakon da mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shugaba Buhari ya ce " ina farin cikin sallamar da aka yi maka daga asibiti bayan samun lafiya musamman a wannan zamani na annoba da hankali ke tashi idan mutum ba shi da lafiya."

An dai kwantar da Sarkin Daura, Umaru Farouk a asibitin gwamnati da ke Katsina ranar Talata sakamakon larurar da ba a fayyace ba.

Wata majiya a fadar wadda ba ta son a ambaci sunanta ta shaida wa BBC cewa an fitar da Sarkin ne daga fadarsa da misalin karfe dayan dare na Talata inda aka garzaya da shi zuwa birnin Katsina.

Majiyar ta kara da cewa an kai Sarkin na Daura bangaren kulawar gaggawa na asibitin gwamnatin jihar. To sai an ce Sarkin yana samun sauki.

Kimanin kwanaki uku kenan dai da killace fadar Sarkin Daura bisa fargabar barkewar cutar korona a cikinta.

Gwamna AMinu Masari na Katsina dai ya ce tuni aka dauki samfurin majinar mutum 89 daga fadar domin yin gwaji.