‘Hausawa 12 ne suka kamu da cutar korona a Faransa’

An wallafa

Sarkin Hausawan Turai, Alhaji Sirajo Jankado Labbo ya ce annobar korona ta taba Hausawa mazauna kasar Faransa, inda shi ma yake zaune.

Sarkin na Hausawa ya ce "al'ummar Hausa da annobar nan ta shafa sun kai 12 inda 11 suka warke amma mutum daya ya rasu."

Ya kara da cewa kawo yanzu dai iya alkaluman da suka samu kenan amma za su ci gaba da bincike domin sanin ko akwai wasu da annobar ta shafa.

"Duk da cewa binciken da muke yi ya samu tazgaro sakamakon kulle amma yanzu tunda an bude za mu ci gaba da binciken kuma za mu sanar da jama'a idan mun samu karin alkaluma."

Dangane kuma da halin da Hausawan mazauna Faransa suka shiga sakamakon dokar kulle a kasar, Sarki Jan Kado ya "Yanzu mutanenmu kowa na cikin walwala saboda kafin dage dokar, idan mutum zai fita dole sai ya rike takardar shaidar wurin da za shi idan ba haka kuma sai an ci mutum tarar euro 135. Amma yanzu koya yana walwala."

A ranar Litinin ne dai Faransa ta fara bude makarantu domin ci gaba da karatu bayan da aka bubbude shaguna da dage dokar hana yawo.

To sai dai Sarkin na Hausawa ya ce "har yanzu mu yaranmu ba su koma makaranta ba kasancewar mutum yana da zabi ko dai yaronsa ya koma yanzu ko kuma karshen wata. Mu mun bari sai karshen wata saboda tsoron sake barkewar cutar karo na biyu."

An dai ja kunnen makarantu a Faransa da ka da su sanya dalibai fiye da 15 a kowanne domin gujewa cunkoso.

Yanzu haka ana ci gaba da sassauta dokar hana fita da harkokin yau da kullum a yawancin sassan nahiyar Turai.