Yau ce ranar ma'aikatan jinya ta duniya

An wallafa

A yayin da ake ci gaba da fama da annobar korona a duniya, yau Talata ce ranar ma'aikatan jinya ta duniya.

Wannan ranar ce kuma ranar da ake tuna wa da cika shekaru 200 da haifar Florence Nightingale- wata ma'aikaciyar Jinya 'yar Burtaniya da ta taimaka wa sojoji a lokacin yakin Crimea.

Kungiyoyin da ke wakiltar ma'aikatan Jinya sun nuna damuwarsu kan yadda ake musu a wannan lokaci da duniya ke fama da annoba har a kasashen da ake gani suna da arziki.

Sun ce akwai gazawa wajen gwaje-gwaje a asibitoci da karancin kayayyakin kariya wato PPE, da kuma rashin tallafa musu a bangaren lafiyar kwakwalwa saboda damuwar da suke shiga, ganin sune a gaba-gaba a wannan yakin.

Kungiyar ma'aikatan jinya ta duniya ta yi gargadi cewa suna cikin hadarin karar da ma'aikatansu a lokacin da duniyar tafi bukatarsu.

Har wa yau, ita ma kungiyar ma'aikatan lafiya da ungozoma reshen jihar Kano ta koka cewa mutanenta 68 sun kamu da cutar korona sakamkon rashin kayan aiki da kuma boye bayanai da marasa lafiya ke yi.