Coronavirus: An debo 'yan Najeriya daga London

An wallafa

Wasu daga cikin 'yan Najeriya 270 da suka sauka a filin jirgin sama na Jihar Legas daga Landan sun shaida wa BBC cewa sun yi jiran awanni ba tare da sanin yadda za su yi ba.

Da yake magana a taron manema labarai ranar Litinin, Ministan Harkokin Wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya ce za a debo 'yan Najeriya mazauna kasashen waje sannan za a killace su na tsawon mako biyu a Abuja, babban birnin kasar.

Sai dai da suke magana da BBC bayan saukarsu a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas, wasu daga cikinsu sun ce tun bayan saukarsu da misalin karfe 1:30 na ranar Juma'a babu wanda ya tarɓe su.

Sun yi korafin cewa kusan 90% daga cikinsu mazauna Jihar Legas ne kuma za su fuskanaci matsala yayin komawarsu Legas din idan wa'adin killacewarsu ya kare saboda haramcin tafiye-tafiye tsakanin jihohi.

Komawarsu kasar na zuwa ne 'yan kwanaki bayan wani jirgin ya sauke wasu 256 daga Daular Larabawa.