Coronavirus: Haihuwa a jirgi ta kawo tsaikon dawo da 'yan Najeriya daga Dubai

Jirgin da ya kwaso 'ƴan Najeriya daga Dubai ya koma bayan wata mata ta haihu a cikinsa jim kaɗan da tashinsa zuwa Legas.
Sanarwar da hukumar da ke kula da 'ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta fitar, ta ce matar ta haifi namiji a cikin jirgin Emirates da ke ɗauke da 'ƴan Najeriya, minti 30 bayan ya baro Dubai.
Wannan ne ya tilastawa jirgin komawa Dubai, a cewar sanarwar.
Ta kara da cewa, matar tana asibiti yanzu haka ana kula da lafiyarta da ta jaririnta waɗanda ke cikin ƙoshin lafiya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Sanarwar ta ce an sauya jirgin, kuma yana kan hanya zuwa Legas ɗauke da ƴan Najeriya 265.
A ranar Talata ne ma'aikatar ƙasashen waje ta Najeriya ta ce za ta fara kwashe ƴan kasar da suka maƙale a wasu ƙasashe sakamakon hana tafiye-tafiye saboda annobar korona.
Ta ce za a kwaso tawagar farko ta 'yan Najeriya 265 ne daga Dubai a ranar Laraba, sannan kuma a kwaso mutum 300 daga Landan.







